Rikici: Mata ta kai karar TikTok saboda samun matsalar kwakwalwa tsabar kallo a kafar TikTok

Rikici: Mata ta kai karar TikTok saboda samun matsalar kwakwalwa tsabar kallo a kafar TikTok

  • Shahararriyar dandalin bidiyo, TikTok wata mata ce ta kai kara kotu wacce ta ce ta samu rauni a kwakwalwa sakamakon dandalin
  • Candie Frazier ta yi iƙirarin cewa ita da sauran masu daidaita abun ciki suna ciyar da sa'o'i 12 a rana don yin bitar abubuwan da ke tada hankali
  • Kamfanin ya ce ikirarin da matar ta yi ba shi da tushe balle makama kuma bai dace da manufofinsa ba, kuma a kodayaushe yana ba da fifiko ga lafiyar ma’aikatansa

Wata mata da ke bitar bidiyo a dandalin bidiyo na TikTok ta kai kara kotu saboda ta haddasa mata wani ciwon kwakwalwa da aka fi sani da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD).

Matar, ta ce ta sami ciwon ne saboda aikinta shine duba bidiyon da suka hada da zane-zane, abubuwan tashin hankali da ka'idodin makirci da sauran 'hotuna masu tayar da hankali.'

Kara karanta wannan

Neman zaman lafiya: Shugaba Buhari ya jaddada kudurinsa na samar burtali ga Fulani

Matsalar kwakwalwa saboda TikTok
Rikici: 'Yar TikTok ta kai kara kotu, ta bayyana yadda TikTok ya zano mata ciwo | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Candie Frazier, wacce ke zaune a Las Vegas kuma 'yar kwangila ga tushen kamfanin TikTok, ByteDance, ta ce ita da sauran masu bitar galibi suna bata sa'o'i 12 kowace rana suna kallon bidiyoyi masu ban tsoro a kan dandamalin.

Babu tallafi ga lafiyar kwakwalwa

Ta ce kamfanin ya gaza wajen ba su isasshen kariya da goyon bayan kula da lafiyar kwakwalwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar mai shigar da karar, Frazier na kallon bidiyon kisan kare dangi a Myanmar, da harbe-harbe da yawa, da kananan yara da ake lalata da su, da kuma yadda ake kashe dabbobi.

Saboda wannan yanayin da ba a kulawa da shi a kai a kai ga hotuna masu muni da masu tayar da hankali a wurin aikinta, ta samu matsala kuma ta fuskanci mummunan raunin kwakwalwa.

Karar, wacce aka shigar a makon da ya gabata a kotun tarayya na California za ta kara sa ido kan bidiyon da ba su da kyau da kuma duba ayyuka a TikTok.

Kara karanta wannan

Anzo wajen: Twitter ya cika ka'idojin Buhari, bayanai sun fito kan dage doka

Rahoton CNN ya ce dandalin an cewa yana fakewa da sunan gasa da Facebook da YouTube kuma ya samu martani sosai kwanan nan daga masu suka da sauransu bayan ya shahara, musamman a tsakanin matasa yayin kulle-kullen Korona.

Kamfanin TikTok ta kare kanta

TikTok ta bayyana cewa tana kokari don habaka yanayin aiki mai kyau ga ma'aikatanta da na kwangila, tana mai cewa tawagar aminci tana hada gwiwa da kamfanoni kebabbu kan muhimmin aikin taimakawa don kare dandamali da al'ummarta.

Dandalin yada bidiyon ya ce zai ci gaba da kara habaka ayyukan kiwon lafiya ta yadda za su ji ana goyon bayan lafiyar kwakwalwarsu da tunaninsu.

Frazier bata aiki a kamfanin TikTok ko tushensa,tana aiki da kamfani ne a Kanada mai suna Telus International, wanda ke ba da ma'aikatan bitar bidiyo ga TikTok da sauran dandamalin kafofin yada bayanai na zamani.

Wani mai magana da yawun Telus ya ce matar ta nuna damuwa a aikinta a baya amma zargin da ta yi bai dace da manufofin kamfanin ba.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

A wani labarin, wani dan Najeriya ya tuna da irin rawar da ya taka a shekarar 2021 yayin da dauki shafin sada zumunta a matsayin hanyar neman soyayya ta gaskiya.

Idris Gombawa, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya tuno yadda ya hadu da wata kyakkyawar mace a wani kantin magani, amma ya rasa karfin gwiwar yi mata magana.

A cewar mutumin, budurwar ta tuntube shi a shafin Instagram don jin ko shi ne mutumin da ta gani a kantin maganin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.