Abun Tausayi: Wata mata ta hallaka jaririn yar aiki dan wata 5 saboda abu daya
- Wata mata ta shiga hannun yan sanda bisa zargin kashe jaririn yar aikinta ta hanyar hora shi da yunwa a jihar Legas
- Mahaifiyar jaririn ta bayyana cewa uwar gidanta ta kwace mata yaro ne saboda ta gaza biyan bashin kudin asibitin lokacin haihuwarta
- Rahoto ya nuna cewa an samu nasarar amso jaririn amma ya mutu yayin da yake kwance a asibiti
Lagos - Jami'an yan sanda sun yi ram da wata mata, Tina Ogbonnaya, bisa zargin kashe wani jariri dan wata biyar da horon yunwa a jihar Legas.
Premium Times ta rahoto cewa Ogbonnaya ta kwace jaririn daga hannun mahaifiyarsa yar shekara 19, wace take mata aiki a gidanta, kan rashin biyan bashi.
A cewar shugaban wata kungiyar kare hakkin bil adama, (BBI), Harrison Gwamnishu, yar aikin Tina ta bayyana cewa ta gaza biyan bashin uwar gidanta kimanin N200,000, wanda ta biya mata yayin da take asibiti.
Ta ƙara da cewa bayan ta haihu, Ogbonnaya ta fara zaluntarta, wanda ya tilasta mata barin gidan amma uwar gidan ta faɗa mata bata isa ta bar gidan ba har sai ta biya bashin.
Ta shaida wa kungiyar BBI cewa, Ogbonnaya ta kwace jaririnta sannan ta kore ta daga gidan kuma duk wani yunkurin amsar jaririn yaci tura, ya zauna hannunta tsawon lokaci ba tare da shayarwa ba.
Shin ta kai rahoto ga yan sanda tun farko?
A cewar mahaifiyar jaririn, da ta kaiwa yan sanda rahoton lamarin da farko ba su ɗauki mataki ba, amma ta samu an dawo mata da yaronta ta hanyar hukumar jin daɗi da walwala ta jihar Legas.
Matar tace jaririn ya dawo hannunta ne rai hannun Allah, kuma ya mutu ne yayin da ake ba shi kulawa a asibitin uwa da yara, ranar Asabar.
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Shugaban ƙungiyar BBI, ya tabbatar da cewa a halin yanzun ana tsare da Ogbonnaya a caji ofis ɗin yan sanda na Ajah.
Kazalika kakakin yan sanda na jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, bai ɗaga waya ba domin jin cikakken bayani kan lamarin.
A wani labarin na daban kuma miyagun Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja
Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace jami'in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) yayin wani hari kan mutanen yankin Abaji, dake Abuja ranar Asabar.
Yan bindigan sun shiga yankin ne da adadi mai yawa da mutanen su, kuma kai tsaye suka farmaki ofishin jami'an DSS dake yankin.
Asali: Legit.ng