Latest
Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar Kaduna, ta musanta zargin da Nasir El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin Uba Sani na sata.
Babban jigo a jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya, Buba Galadima, ya yi magana kan hadakar da jam'iyyun adawa ke shirin yi don kwace mulki a hannun APC.
An rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu ya saka labule da shugabannin tsaron ne karkashin jagorancin shugaban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa.
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ci gaba da fitar da bayanai kan zargin yunkurin yin lalata da ita da take yi wa Godswill Akpabio.
Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Sarkin Musulmi na shirin musuluntar da Najeriya.
Ministan Abuja, Wike ya kwace filin PDP a Abuja bisa gazawar jam’iyyar na biyan harajin filin tun 2006. FCTA ta ce ta sha jan kunne amma PDP ta ki biyan bashin.
Majalisar wakilai ta Najeriya ta amince da kudirin haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar mata. Majalisar ta amince da kudirin ne bayan ya tsallake karatu na uku.
Kotun Tarayya ta yi zama kan ƙarar kamfanin NNPCL da ke ƙalubalantar cancantar karar da matatar Aliko Dangote ta shigar kan lasisin shigo da kaya a Abuja.
Dan daudu mai shigar mata da ya tsere daga Najeriya ya ce ya bar kasar har abada. Bobrisky ya ce a Najeriya har Sanatoci da ministoci na magana a kansa.
Masu zafi
Samu kari