Latest
Kotun majistare da ke Akure cikin jihar Ondo ta daure wani Fasto shekaru biyu a gidan gyaran hali bisa zargin fasa shago da kuma yin sata a Iwaro Oka Akoko.
Wani miji da matarsa sun fada komar hukumar 'yan sandan jihar Yobe bayan zamba cikin aminci da suka aikata ta hanyar basajar shiga Musulunci, inda suka daukewa.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce tun da Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, ya kamata wadanda ke goyon bayansa su fadi cigaban da ya kawo a shekaru takwas a ofis.
Wani bidiyo ya nuno wasu yan yara suna shiga wani otal. An gano yaron ya dauki yarinya don su kama daki. Bayan zantawa da mai tarbar baki sai suka shige abinsu.
'Yan majalisar Wakilai sun bukaci karin albashi da alawus don rage radadi tun bayan cire tallafin man fetur a kasar, sun bayyana yadda suke cin bashi a wata.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Ekiti da aka sace ya kubuta daga hannun ƴan bindiga. Jami'an tsaro ne suka ceto shugaban na APC da wasu mutum biyu da aka sace.
Dakarun sojoji na atisayen 'Operation Safe Haven' sun yi arangama da miyagun ƴan bindiga a jihar Plateau. Sojojin sun halaka ƴan bindiga uku da kwato makamai.
Da aka yi hira da shi a jiya, Shugaban Kwastam ya shaida cewa iyakoki kadan ne aka bude, akasin abin da ake rahotowa. Iyakoki biyar ne, halin da ake ciki kenan
An yi jana'izar Malam Imam Galadanci, surukin sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, a ranar Laraba bayan dauko gawarsa.
Masu zafi
Samu kari