Latest
Wani ɗan Najeriya ya koka inda ya caccaki bankinsa bayan ya gano cewa makuɗan kuɗaɗen da ya ciro a banki na jabu ne. Kuɗaɗen dai an ba shi su ne a Yuro.
Amurka ta bayyana cewa majalisar dattawan ƙasar da ta amince da naɗin kakadun ƙasar a wasu kasashen duniya ba har kawo yanzu cikinsu harda Najeriya.
Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi za su san makomarsu a Kotun Koli nan da sa'a 24. Alhamis Kotun Koli za ta yanke hukuncin karar zaben Shugaban kasa.
Ana da labari wasu hare-hare da aka kai a a Birnin Gwari, an kashe mutane akalla hudu a jihar Kaduna, inda aka kai hare-haren ba su da nisa da sojojin kasa.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Adamu Fika ya riga mu gidan gaskiya a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba yayin da ya ke dawo wa daga Ingila.
Wani kwastoma ya fusata bayan ya rasa N500,000 a asusun ajiyarsa na banki, keastoman dai ya kinkimi man fetur inda ya yi yunƙurin cinnawa bankin wuta a Ogun.
Malam Uba Sani ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu domin ƙara jan hankalin gwamnatin tarayya ta taimaka wa jiharsa a fannin noma, lafiya da tsaro.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya zargi Isra'ila da saba dokokin jin kai na kasa da kasa yayin da ta ke kai munanan hare-hare kan Gaza.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a gidan wata babbar malamar jami'a ta jami'ar jihar Nasarawa tare da yin awon gaba da ita zuwa cikin daji.
Masu zafi
Samu kari