Latest
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a gidan wata babbar malamar jami'a ta jami'ar jihar Nasarawa tare da yin awon gaba da ita zuwa cikin daji.
Sanatoci sun fara binciken yadda Gwamnati ta kashe Naira Tiriliyan 11 a shekaru 13. An yi ta kashe kudi daga zamanin marigayi Ummaru ‘Yar’adua zuwa yau.
Benjamin Okezie Kalu ya ce bai da alakar siyasa kai-tsaye da Nkeiruka Onyejeocha da za su yi fada. Wadannan manyan ‘yan siyasa sun fito daga jihar Abia.
An bar APC babu ‘Dan takara a zaben Gwamnan Bayelsa, Hukumar INEC ta bi umarnin kotu. Ba a taba 'dan takaran kowace jam'iyya ba illa na APC mai mulki.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun tare hanya a jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane masu yawa. Cikin waɗanda ƴan bindigan suka sace har mai shayarwa.
Farfesa Kingsley Moghalu ya fadi abin da zai jawo Naira ta farfado bayan $1 ta wuce N1200 a BDC, tsohon mataimakin gwamnan CBN ya ba sababbin Gwamnoni shawara.
Sabon shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya umarci dukkan jami'an hukumar daga mataki na 17 zuwa kasa su bayyana kadarorinsu kamar yadda shi ma ya yi.
Wani magidanci ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa a jihar Benue bayan ya caccaka mata wuƙa a jiki. Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar mummunan lamarin.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin kaca-kaca da ƴan ta'adda a jihar Sokoto. Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda masu yawa tare da ƙwato makamai.
Masu zafi
Samu kari