'Yar Fim, Halima Sabuwa Ta Rasu ana Gobe Sallah bayan Shiga Matsalar Rayuwa

'Yar Fim, Halima Sabuwa Ta Rasu ana Gobe Sallah bayan Shiga Matsalar Rayuwa

  • Tsohuwar jarumar fim da aka fi sani da Halima Sabuwa ta rigamu gidan gaskiya 'yan watanni bayan fitowa tana neman taimakon al'umma
  • A kwanakin baya jarumar ta fito tana cewa ta shafe sama da shekara 20 tana fim amma bata cimma wani abin karki a rayuwarta ba gada daya
  • Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da tarihin rayuwar fim da Sabuwa ta yi, musamman kalubalen da ta fuskanta a Kannywood

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Al'umma da dama sun fara jimami bayan sanar da rasuwar tsohuwar jarumar Kannywood, Halima Sabuwa da ta shafe shekaru tana fim.

A kwanakin baya dai jarumar ta fito tana nuna cewa tana fama da matsalolin tattalin arziki duk da shafe shekaru da ta yi a masana'antar Kannywood.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Halima Sabuwa da ta rasu
Marigayiywa Halima Sabuwa a wajen wani taro. Hoto: Halima Atete
Source: Facebook

Za a yi jana'izar Halima Sabuwa

Fitacciyar jarumar Kannywood, Halima Atete ce ta sanar da rasuwar Halima Sabuwa a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa za a yi janaʼizar Sabuwa a yau Ahamis 19 ga Maris 2026 a unguwar Dan Maliki a karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano.

Tarihin Sabuwa a Kannywood

A wata hira da Muryar Amurka, Halima Sabuwa a shirin fim na Dadin Kowa, ta ce ta fara harkar fim shekaru 20 da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa Sabuwa ta ce ta shiga shirin fim na Dadin Kowa ne domin fadakarwa da ilmantar da alu’umma dangane da kalubalen rayuwa a yanzu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin da ya sa 'yan ta'adda suka tayar da bam a Maiduguri

Ta ce ta fito a matsayin Sabuwa matar Malam Ayuba mai gadi, mace mai hakuri da kuma yarda da kaddara, wacce take tarbiyartar da dan ta Dan Asabe kan tafarkin da ya dace, da bashi tarbiya wajen bin biyayya da rashin raina sana’a.

Kalubalen da Sabuwa ta fuskanta

Daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta a shirin Dadin Kowa ta ce baya wuce fita sassafe da suke yi domin gudanar da aikinsu, sannan da zarar ta fita mutane su kan yi tururwa domin su ganta.

A wani bidiyo da Kano Online News ya wallafa a Facebook a Janairun 2026, Sabuwa ta bayyana cewa ta shekara 20 a fim amma a yanzu ko na abinci ma da kyar ta ke samu.

Ta ce:

'Wani lokacin haka muke kwana da yuwa, ga rashin lafiya'

Kara karanta wannan

Abin da ake cewa kan Trump ya gargadi Tinubu bayan harin Maiduguri

A bidiyon, ta bayyana cewa tana neman taimakon al'umma domin a lokacin bata da gidan da za ta zauna ga shi tana da yara sosai kuma ba su da abin yi.

Marigayiya Halima Sabuwa
Marigayiya Halima Sabuwa na wani jawabi. Hoto: Halima Ateta
Source: Facebook

Cikin bayanin da ta yi, ta ce ta fita a harkar fim baki daya, duk da cewa ta taba cewa a lokacin da ta fara fim sai da iyayenta suka sanya hannu a takarda kafin a amince mata ta zama jaruma.

'Yan Kannywood da suka mutu

A wani labarin, Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen wasu jarumar Kannywood da suka rigamu gidan gaskiya a shekarar 2025.

Wasu daga cikin jarumar sun rasu ne bayan doguwar rashin lafiya yayin da wasu kuma suka rasu saboda haduran mota a kan titunan kasar nan.

Daga cikin wadanda muka tattaro muku a rahoton akwai Malam Nata'ala, Maijidda Muhammad da aka fi sani da Fulani da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng