Samha Inuwa: Kotu Ta Yanke wa Fitacciyar Jarumar Kannywood Hukuncin Ɗaurin Wata 6
- Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta tura jarumar Kannywood Saadatu Mohammed Inuwa gidan yari na watanni shida
- Jarumar wadda aka fi sani da Samha ta amsa laifinta na goge hancinta da takardar naira 'yan dubu dubu a shekarar 2020
- Mai shari'a S.M Shuaibu ya ba jarumar zabin biyan tarar dubunnan daruruwan Naira maimakon zuwa kurkuku bayan ta nuna nadama
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Babbar Kotun Tarayya dake zaman ta a birnin Kano, ta yanke wa jarumar Kannywood, Saadatu Mohammed Inuwa, hukuncin zaman gidan yari na watanni shida.
Mai Shari’a S.M Shuaibu ne ya karanta hukuncin a yau Juma’a, bayan samun 'yar wasar hausan da laifin wulakanta takardar kudin Najeriya, watau Naira.

Source: Instagram
Tuhumar da ake yi wa jaruma Samha

Kara karanta wannan
Lamari ya juya: Ƴan bindiga sun yi saɗaf saɗaf sun hallaka 'DPO' bayan sace shanu
A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, EFCC ta ce ta gurfanar da jarumar, wadda aka fi sani da Samha, bisa zarginta da keta dokokin babban bankin Najeriya na shekarar 2007.
An karantawa Samha tuhumar da ake yi mata, da cewa:
"Ke Saadatu Mohammed Inuwa, a wani lokaci a shekarar 2022, kin wulakanta takardun N1,000 ta hanyar goge hancinki da kudin a fili.
"Wannan mataki da kika dauka ya saba wa sashi na 21a, karamin sashi na 1, na dokar babban bankin Najeriya ta shekarar 2007."
Bayani kan shari'ar jaruma Samha
A lokacin da aka karanta mata tuhumar, jaruma Samha Mohammed ta amsa laifinta ba tare da ta yi wata ja'in'ja ba.
Sakamakon amsa laifin, lauyan masu shigar da kara, Musa Isah, ya bukaci kotun da ta yanke mata hukunci daidai da tanadin dokokin kasar Najeriya.
Lauyan ya bayyana cewa matakin zai zama darasi ga sauran mutane wadanda ke da dabi'ar wulakanta kudin kasar a wuraren taro ko kuma bidiyoyi.
Sanarwar EFCC ta ce:
"Jarumar ta roki kotu da ta yi mata sassauci bisa wannan laifi da ta aikata, tana mai cewa wannan ne karon farko da aka taba kamata da irin laifin, kuma ta yi nadamar abin da ta aikata."

Source: Facebook
Hukuncin da kotu ta yankewa Samha
Bayan sauraron kowane bangare, Mai Shari'a Shuaibu ya yanke wa Samha Inuwa hukuncin watanni shida a gidan yari, amma ya ba ta zabin biyan tara ta N200,000.
Wannan hukunci na zuwa ne a matsayin wani bangare na kokarin hukumomi na tabbatar da darajar kudin naira a hannun daukacin yan kasar Najeriya.
Shari'ar ta jawo hankalin mutane da dama a dandalin sada zumunta, musamman masoyan jarumar dake jihar Kano da sauran sassan kasar nan baki daya.
Karanta sanarwar EFCC kan hukuncin kotun a kasa:
EFCC ta kama Samha M Inuwa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, EFCC ta cafke jaruma Samha Inuwa a Jihar Kano bisa zargin goge majina da takardun kudin Naira a cikin wani bidiyo.
'Yar wasar kwaikwayon tana tsare a ofishin hukumar yayin da ake gudanar da bincike kafin a gurfanar da ita a gaban kotun tarayya nan kusa.
Wannan kamu na nuna kudurin EFCC na kare darajar kudin kasar Najeriya da kuma hukunta duk wanda aka samu yana wulakanta Naira.
Asali: Legit.ng
