‘Daya Muke da Su’: Dan Wasan Kannywood Ya Kwatanta Kansu da Malaman Musulunci

‘Daya Muke da Su’: Dan Wasan Kannywood Ya Kwatanta Kansu da Malaman Musulunci

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Al’amin Buhari, ya bayyana cewa masana’antar fim na fuskantar rashin fahimta daga malamai
  • Al’amin ya ce saƙon gargadi da ‘yan fim ke bayarwa ya yi daidai da na malamai, sai dai ana nuna shi ne ta hanyar wasan kwaikwayo
  • Jarumin ya kara da cewa mutane da yawa sun fi son kallon fim mai darasi fiye da sauraron wa’azi, lamarin da ke jawo ce-ce-ku-ce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Fitaccen dan wasan kwaikwayo a masana'antar Kannywood, Al'amin Buhari ya magantu kan bunkasa sana'arsu da suke yi.

'Dan wasan kwaikwayon ya bayyana irin kalubale da suke fuskanta wanda ya yi fatan samun ci gaba game da masana'antar ta su.

Jarumin Kannywood ya kwatanta kansu da malaman addini
Dan wasan Kannywood, Al'amin Buhari. Hoto: @officialalameenbuhari.
Source: TikTok

Al'amin Buhari ya ja hankalin mutane

Jarumin ya bayyana haka ne a faifan bidiyo da RFI Hausa ta yi hira da shi wanda ta wallafa a shafinta na X a jiya Laraba 28 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi tone tone kan Abba, ya fadi alherin da Buhari ya masu

Ya bayyana yadda gwamnotocin baya musamman na Goodluck Jonathan ta taimakawa masana'antar duk da cewa shi dai bai samu ba.

Ya ce:

"Wato tsakani da Allah, Kannywood tana da makiya daban-daban, dalili kuwa kowa da irin fassarar da yake yi wa yan wasan Kannywood.
"Wasu na kallonmu a kan daidai, wadanda kuma ba su yi mana kallon daidai kusan su ne abokan fadanmu.
"Dalili kuwa shi ne yau za ka ga malami ya kafa mimbari yana wa'azi yana cewa idan mutum ya yi kaza sakamakonsa kaza ne haka abu kaza ba kyau, shi kuma dan fim idan ya dauko labarinsa zai ce ga wannan ba shi da kirki, sai ka ga karshensa ba kyau."
Dan wasan Kannywood ya fadi wa'azin da suke yi al'umma
Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kannywwod. Hoto: Abba El-Mustapha.
Source: Facebook

'Abu daya muke yi da malamai': Jarumin Kannywood

Dan wasan Kannywood ya ce kusan duka gargadi daya suke yi da malaman amma an fi daura soyayya ga malaman saboda su yan fim a wasan kwaikwayo suke yi.

"Akwai rashin fahimta tsakaninmu da malaman da kuma ma yan kallo gaba daya, idan da za a zauna a fahimci juna za a ga duk abin da ake yi daya ne.

Kara karanta wannan

Ilhan Omar: Bidiyon yadda aka farmaki 'yar majalisar Amurka a taron jama'a

"Bambancin daya ne, mu muna saka yi a matsayin wasan kwaikwayo sabanin yadda su malamai ke yi."

- Al'amin Buhari

Al'amin Buhari ya kara da cewa da yawa daga cikin mutane sun fi son kallon fim da yake da alaka da abin da malamai ke cewa madadin sauraron wa'azin.

'Don akida na shiga fim': Dan wasan Kannywood

A baya, kun ji cewa dan wasan Kannywood, Malam Inuwa Ilyasu, ya bayyana cewa ya shiga harkar fim ne domin fadakar da jama'a da kuma koyar da addinin Musulunci.

A cewar Malam Inuwa, bai zabi fitowa a matsayin malami a fina-finai ba, sa'a ce kawai ta sa yana samun waɗannan ɓangare wanda kuma yana jin dadin haka.

Ya ce masana'antar fim ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan matasa, musamman wurin koyar da ɗabi'a, tarbiyya da kuma al'adar Hausawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.