Fitacciyar Jarumar Fim a Najeriya na cikin Mawuyacin Hali, Ta Ce Za Ta Iya Mutuwa

Fitacciyar Jarumar Fim a Najeriya na cikin Mawuyacin Hali, Ta Ce Za Ta Iya Mutuwa

  • Jarumr fim a Najeriya ta bayyana mawuyacin halin da Fasto Chris Okafor ya jefa ta a ciki bayan tsawon lokaci suna soyayya da alkawarin aure
  • Jaruma Doris Ogala ta ce saboda Fasto Okafor ta kashe aurenta duk da dama ba jin dadin zama da tsohon mijinta take ba
  • Ta kuma bayyana wasu ibtila'i da suka fada mata, kama daga zubar da ciki, bari da tashin hankalin da ta fuskanta a zaman aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Fitacciyar jarumar Nollywood, Doris Ogala, ta bayyana damuwa cewa watakila ba za ta daɗe a raye ba sakamakon abin da ta kira “munanan abubuwa” da Fasto Chris Okafor ya yi mata.

Jarumar fim din ta fashe da kuka a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ta ce komai ba ya tafiya daidai a rayuwarta.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Iran da Amurka sun nuna wa juna yatsa a taron tsaro na duniya

Jaruma Doris Ogala.
Fitacciyar jarumar Nollywood, Dorslis Ogala Hoto: Doris Ogala
Source: Instagram

A faifan bidiyon da wani Chuka Erice ya wallafa a X, jaruma Ogala ta yi magana kan raɗaɗin da ta sha na zubar da ciki sau da dama, da kuma yadda ta rika ganin likitoci suna cire mata jariri daga mahaifa.

Wane hali jaruma Doris Ogala ke ciki?

Haka kuma, ta koka kan cin amanar aure, tana cewa ba abu ne mai sauƙi mace ta koma gida ta tarar da wata mace a ɗakin aurenta, ko kuma ta rayu a cikin aure mai cike da tashin hankali.

Jarumar ta ce:

“Mutane suna tunanin ya kamata na zama mai juriya, wasu kuma suna zaton wasan kwaikwayo ko ƙirƙirar abun magana kawai nake yi, suna ganin komai lafiya, alhali ba haka ba ne.
“Ba daidai ba ne mace ta zubar da ciki ko ta yi bari sau da dama, ko ta ga likitoci suna cire mata jariri, ko a riƙa kama ta ana kullewa. Ba na jin dadin rayuwar nan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Matar aure ta yi amfani da adda, ta kashe mijinta da budurwarsa

“Ba daidai ba ne mace ta koma gidanta na aure ta tarar da wata mace a ɗakinta, ko ta rayu a cikin aure mai raɗaɗi da babu zaman lafiya, komai ba ya tafiya daidai.”

Soyayya ta jefa jarumar fim a wahala

Doris Ogala ta zargi Chris Okafor, wanda ya kafa cocin Mountain of Liberation and Miracle Ministries, da aikata mata abubuwan da za su iya hana ta yin magana.

“Watakila ba zan daɗe a raye ba. Chris Okafor ya yi mini abubuwa marasa kyau da yawa. Na gaji da jurewa. Komai ba ya tafiya daidai. Ina roƙon ɗan uwana Emeka, idan zai iya, ya taimaka mini,” in ji ta.

Rikicin da ke tsakanin Ogala da Okafor ya ɓarke ne makonni da suka wuce bayan wani bidiyon neman aure na faston da wata mata mai suna Pearl Okafor ya bayyana a intanet.

Ogala ta yi zargin cewa tun 2017 take soyayya da Okafor, tana mai cewa ta kashe aurenta ne saboda shi. Ta kuma zarge shi da cin amanarta bayan shekaru na soyayya da alƙawarin aure, in ji jaridar The Cable.

Jaruma.Ogala da Fasto Okafor.
Fitacciyar jarumar Nollywood, Doris Ogala da Fasto Chris Okafor Hoto: Doris Ogala
Source: Instagram

Auren jarumar Nollywood, Anita ya mutu

Kara karanta wannan

Daga Urumba zuwa Uromi: Yadda ake yi wa Hausawa kisan gilla a Kudancin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa fitacciyar jarumar Nollywood, Anita Joseph, ta bayyana cewa aurenta da Fisayo Michael da aka fi sani da MC Fish Michael ya zo ƙarshe.

Jarumar ta ce wannan lokaci ne da ya sa ta tsaya ta yi nazari mai zurfi a kan kanta da abubuwan da ke kewaye da ita kafin ta yanke hukuncin rabuwa da mijinta.

Bayaninta ya kawo karshen jita-jita da suka dade suna yawo game da halin da aurensu ke ciki, musamman a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262