Abin da Adam Zango Ya Ce bayan Kyautar Dalleliyar Mota daga Kashim Shettima

Abin da Adam Zango Ya Ce bayan Kyautar Dalleliyar Mota daga Kashim Shettima

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ba fitaccen ɗan Kannywood Adam A. Zango kyautar mota
  • Adam A. Zango ya bayyana farin cikinsa, inda ya gode wa Sanata Shettima bisa karamci, yana mai cewa hakan ya nuna tausayi da nagartarsa
  • Jarumin wasan kwaikwayon ya yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasa addu’o’in lafiya da nasara, yayin da masoyansa suka taya shi murna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ba Adam A Zango kyauta ta musamman.

Kashim Shettima ya gwangwaje dan wasan Kannywood din ne da kyautar dalleliyar mota domin ci gaba da gudanar da harkokinsa.

Kashim Shettima ya ba Adam A Zango kyautar mota
'Dan wasan Kannywood, Adam A Zango da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Adam A Zango, Kashim Shettima
Source: Facebook

Adam A Zango ya godewa Kashim Shettima

Hakan na cikin wani rubutu da mawakin ya yi a shafinsa na Facebook a jiya Alhamis 8 ga watan Janairun 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Rikicin Ribas: Ministan Abuja ya debo da zafi, ya kira gwamna da 'mara tarbiyya'

'Dan wasan Kannywood ya yi godiya ta musamman ga tsohon gwamnan Borno tare da nuna farin cikinsa game da kyautar.

Adam Zango ya kuma bayyana jin dadinsa game da yadda da mataimakin shugaban kasar ya nuna masa halacci a halin da ake ciki.

Har ila yau, ya yi wa Sanata Kashim Shettima addu'o'i na musamman domin ci gaba da samun lafiya, hikima da nasara a rayuwarsa.

A cikin rubutun da ya yi a dandalin Facebook, Zango ya ce:

"Mai Girma,
"Kyautarka ta nuna halin tausayi da nagartar jagorancinka tare da jajircewarka wajen kula da jin daɗin ’yan Nijeriya.
"Na yi matuƙar jin daɗin wannan karamci, kuma ina mika godiya ta musamman bisa goyon bayan da ka nuna mini.
Mai Girma, Kashim Shettima, nagode ƙwarai da amincewa da ka yi mini, Ina roƙon Allah ya ba ka lafiya, hikima, farin ciki da nasara a ci gaba da hidimtarka ga ƙasarmu mai albarka."
Adam A Zango ya yi godiya ga Shettima bayan kyautar mota
Dan wasan Kannywood, Adam Zango. Hoto: Adam A Zango
Source: Facebook

Martanin mutane kan kyautar Shettima

Mutane da dama sun bayyana farin cikinsu game da kyautar da aka ba Zango inda suka yi ta masa addu'o'i.

Kara karanta wannan

Kananan yara 469 sun mutu a jihar Kano, bincike ya nuna abin da ya kashe su

Wannan kyauta da aka ba Adam A Zango ta faranta masoyansa wadanda suka taya shi murna kwarai da gaske.

Shamsudden Abubakar:

"Masha Allah, ina maka fatan samun motoci a da yawa gidanka, muna jiran mota kirar G-Wagon."

Bashar AY Muhammad:

"Ina taya ka murna, amma ADC za ta zo domin ceto Najeriya a 2027 da yardar Allah."

Smart Ahmad:

"Da wannan nasara, za a samu kalubale da yawa a rayuwa, ka tunkare su da karfin guiwa da jajircewa, ina maka murna."

Bala Bakasan Wani Yasamu:

"Allahu Akbar, duk da ba ni son a samu amma yadda ka san ni an ka ba tun da an bai wa masoyina, Allah shi sanya maka alheri Usha ya tsare hanya."

Abba Kabir ya ba mawaki kyautar mota

A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gwangwaje daya daga cikin mawakan da suka yi masa hidima a lokacin yakin zabe.

Mawakin da aka sani da Shalelen Mawaka, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ya samu kyautar sabuwar mota daga gwamnan.

Mutane sun yi dafifi a kasan hoto da bidiyon motar da mawakin ya wallafa, inda su ke yiwa Gwamna Abba godiya kan karamcinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.