Zaman Gidan Miji Ya Kare: Auren Jarumar Fim a Najeriya Ya Mutu

Zaman Gidan Miji Ya Kare: Auren Jarumar Fim a Najeriya Ya Mutu

  • Fitacciyar jarumar Nollywood, Anita Joseph, ta bayyana cewa aurenta da Fisayo Michael da aka fi sani da MC Fish Michael ya zo ƙarshe
  • Rahotanni sun bayyana cewa jarumar ta ce ta yanke wannan shawara ne bayan dogon lokaci tana tunani da neman samun sauki
  • Bayaninta ya kawo karshen jita-jita da suka dade suna yawo game da halin da aurensu ke ciki, musamman a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Anita Joseph, ta tabbatar da cewa aurenta da mijinta, Fisayo Michael, MC Fish, ya zo karshe, lamarin da ya kawo karshen rade-radin da suka shafe watanni suna yawo a kafafen sada zumunta.

Anita Joseph ta ce ta samu sauki bayan shiga wani yanayi na radadi, tana mai jaddada cewa duk da ba ta da amsar dukkan tambayoyin jama'a.

Kara karanta wannan

ICPC ta jero ma'aikatun da aka fi tsammanin badakala a Najeriya a 2025

Anita Joseph da mjinta da suka rabu
MC Fish da Anita Joseph da suka rabu. Hoto: @anitajoseph
Source: Instagram

Jarumar ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce lamari ne mai girma.

Auren jarumar fim, Aninta Joseph ya mutu

A sakon da ta wallafa, Anita Joseph ta bayyana cewa rayuwa, musamman aure, na gwada karfin mutum ta hanyoyi da ba a zata ba.

Ta ce wannan lokaci ne da ya sa ta tsaya ta yi nazari mai zurfi a kan kanta da abubuwan da ke kewaye da ita.

Ta rubuta cewa:

“Rayuwa na gwada karfinmu ta hanyoyi da ba mu zata ba, musamman a cikin aure.
"A wannan lokaci na kasance ina tunani mai zurfi, jin radadi da neman warkewa.”

Vanguard ta wallafa cewa jarumar ta kara da cewa ba ta da cikakkun amsoshi da za a yi mata, kuma ta yanke shawarar rungumar hakuri, juriya da imani, tana tafiya sannu a hankali zuwa wani sabon babi na rayuwarta.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci, Sheikh Guruntum ya yi nasiha a kayar da masu mulki a 2027

Anita Joseph da mijinta da suka rabu
Anita Joseph da mijinta kafin su rabu. Hoto: @anitajoseph
Source: Instagram

A karshen sakon, Anita Joseph ta bayyana karara cewa aurenta ya zo ƙarshe, kalaman da suka tabbatar wa mabiyanta cewa rabuwar ta zama gaskiya, ba jita-jita ba.

Rade-radin da ya dabaibaye auren jarumar

Tsawon watanni kafin wannan bayani, an dade ana rade-radin cewa auren Anita Joseph da MC Fish ya samu matsala.

Jita-jitar sun hada da zargin rashin aminci, tashin hankali a cikin gida da kuma matsalolin shaye-shaye da ake alakanta wa mijinta.

Haka kuma, wasu rahotanni da ke yawo sun ce Anita Joseph ta fuskanci matsalolin haihuwa, ciki har da bari, lamarin da ya kara jawo tausayin jama’a da muhawara a shafukan sada zumunta.

Sai dai duk da wadannan jita-jita, jarumar ta kasance tana kauce wa yin bayani kai tsaye kan halin aurensu, tana mai cewa tana cikin koshin lafiya, tare da rokon jama’a su mutunta sirrinta.

Anita Joseph da Fisayo MC Fish Michael sun daura aure ne a shekarar 2020, bikin da ya ja hankalin jama’a da dama a masana’antar Nollywood da masu sha’awar fina-finai.

Kara karanta wannan

Tarihin gwamna Umo Eno da ya sha azaba yana talla kafin samun arziki

Falasdinawa 54 sun daura aure a Gaza

A wani rahoton, kun ji cewa an yi wani taro a Gaza inda daruruwan Faladinawa suka taru domin shaida gagarumin biki da aka yi.

'Yan uwa da abokan arziki sun taru a Gaza domin bikin sama da mutum 50 da suka angwance bayan tsagaita wuta da kasar Isra'ila.

Legit Hausa ta ta samu bayanai cewa wata gidauniya ce ta tallafa musu da kudi da kayayyaki kasancewar sun tafka asara a hare-haren da aka kai musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng