Mai Wushirya: Mansurah Isah Za Ta Dauki Mataki kan Mata Sharri game da Aurensa

Mai Wushirya: Mansurah Isah Za Ta Dauki Mataki kan Mata Sharri game da Aurensa

  • Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ta nuna damuwa kan yi mata sharri game da auren dan TikTok, Ashiru Idris (Mai Wushirya)
  • Mansurah ta ce labarin karya da wata jaridar yanar gizo ta wallafa a kan ta ya jefa ta da iyalanta cikin damuwa da tashin hankali
  • Ta ce ta ba ta awanni 24 ta cire labarin bogi da ta wallafa, amma har bayan kwana uku ba ta yi hakan ba, duk da sun nemi afuwa a waya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohuwar yan wasar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana halin da ta shiga bayan yi mata sharri da wata jaridar yanar gizo ta yi.

Mansurah Isah ta ce sharrin da aka yi mata ya jefa ta cikin zullumi da ita da iyalanta inda ta tabbatar da cewa za ta dauki mataki.

Kara karanta wannan

Hisbah ta soke shirin auren Mai Wushirya da 'Yar Guda, an ji dalili

Mansurah Isah za ta dauki mataki kan bata mata suna
Dan TikTok, Mai Wushirya da Mansurah Isah. Hoto: Mansurah Isah, Mai Wushirya.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani rubutun gargadi da ta yi a shafin Facebook a jiya Litinin 27 ga watan Oktobar 2025 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin jaridar ta wallafa kan Mansurah Isah

Hakan ya biyo bayan wallafa wani rahoto da jaridar yanar gizo mai suna AMC Hausa ta yi game da aurenta da Mai Wushirya.

Rahoton ya ce Mansurah Isah ta ce ta shirya auren Mai Wushirya idan har yana sonta tsakani da Allah.

Mai Wushirya ya yi kaurin suna a shafukan sadarwa a kwanakin nan bayan kotu ta ba da umarnin hada shi da Yar Guda aure kafin daga bisani Hisbah ta yi watsi da umarnin.

Hisbah ta fasa auren Mai Wushirya da Yar Guda
Hoton Yar Guda dan TikTok, Mai Wushirya a Kano. Hoto: Mai Wushirya.
Source: Facebook

Matakin da Mansurah ke shirin dauka

Tsohuwar matar Sani Danja ta bayyana cewa kwana uku ta ba jaridar ta sauke labarin kafin ba ta hakuri a waya saboda bata mata suna.

Ta ce:

"Na ba ku awa 24 ku sauke labarin bogi da kuka yi a kai na, na ce ku cire ku ba ni hakuri, yau kwana uku kenan ba ku yi hakan ba.

Kara karanta wannan

Fashewar tankar mai a Neja: Tinubu ya aika sako ga iyalan mutum 30 da suka mutu

"Bayan kun kirani a waya kun bani hakuri, na ce muku Ina cikin dawainiya na shirin 'WalkAwayCancer' da muke shiryawa."

Mansurah Isah ta ce abin takaici ne yadda aka yi kokarin bata sunanta inda ta kalubalanci inda ta fadi wannan magana.

Ta ce wannan rahoton karya da aka yada ya zubar mata da kima da kuma sanya iyalanta cikin kunci da rudani.

"Duk wani abu da zan Iya muku na yi, amma ku sani, yanzu Ina da lokacin ku. kwana uku kun yi maganar karya akaina, kun zubar min da kima.
"Kun hana ni barci da jin dadi da walwala, kun saka iyalaina cikin rudani akan kazafin karya da kuka yi min. In Allah ya yarda za ku ji daga gare mu."

- Mansurah Isa

Mai Wushirya ya fasa auren Yar Guda

Mun ba ku labarin cewa tun kafin magana ta yi nisa, shahararren dan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya kawo cikas a batun aurensa da Basira 'Yar Guda

Kara karanta wannan

Damina ba ta kare ba: Ruwan sama zai sauka a Taraba, Kogi da wasu jihohin Arewa

Mai Wushirya ya bayyana cewa bai da wata masaniya kan kudin gudunmawa da ake karba da sunan aurensa da 'Yar Guda.

Ya bayyana cewa tun da farko tsoro ne ya sanya ya amince da cewa zai auri 'Yar Guda wadda suke fitowa a cikin bidiyoyi tare da ita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.