Mutuwa Ta Girgiza Masana'antar Fim a Najeriya, Fitaccen Jarumi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Ta Girgiza Masana'antar Fim a Najeriya, Fitaccen Jarumi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood ta sake shiga jimami bayan rasuwar daya daga cikin manyan jarumanta, Duro Michael
  • Rahotanni sun nuna cewa Jarumi Michael ya mutu yana da shekaru 67 da haihuwa bayan fama da doguwar rashin lafiya
  • Furodusa a masana'antar Nollywood, Stanley Ontop ya tabbatar da rasuwar jarumin, ya soki yadda 'yan wasan ba su taimakon juna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta Kudancin Najeriya watau Nollywood, Duro Michael ya riga mu gidan gaskiya.

Fitaccen jarumin fina-finan ya rasu yana da shekaru 67, lamarin da ya sake jefa masana’antar Nollywood cikin jimami da alhini.

Jarumin Nollywood, Duro Michael.
Hoton fitaccen jarumin Nollywood a Najeriya, Duro Michael. Hoto: Fortune Nwodika
Source: Facebook

Ƙwararren mai shirya fina-finai a Nollywood, Stanley Ontop, ne ya tabbatar rasuwar jarumin yau Juma'a, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bayan sanar da rasuwar abokin aikin na su, furodusan ya yi tir da yadda ’yan Nollywood ba sa taimakon junansu musamman idan wani ya shiga halin jarabawa.

Kara karanta wannan

Martanin da Sarki ya yi bayan zargin Peter Obi da rashin mutunta shi a sakon taya murna

An tabbatar da mutuwar Jarumi Michael

Stanley Ontop ya bayyana cewa Michael ya mutu ne kwanaki kaɗan da suka gabata bayan ya sha fama da wata cuta mai tsanani.

Ya rubuta cewa:

“Fitaccen jarumin Nollywood, Duro Michael, ya mutu. Ya rasu ne kwanaki kaɗan da suka wuce bayan fama da cuta mai tsanani.
"Allah ya jikansa, mu na fatan ya huta lafiya. Omo, duk da haka, mun kasa taimakon kanmu a cikin masana'antar Nollywood, abin ba daɗi amma babu haɗin kai a tsakaninmu."

Yadda jarumin na Nollywood ya sha fama da jinya

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya dade yana kwance ba shi da lafiya, amma bai samu tallafi daga abokan sana'arsa na masana'antar Nollywood ba.

Ana ganin wannan dalili ne ya sa Furodusa Stanoey Ontop ya nuna damuwa kan yadda jarumai ba su iya taimakon junansu.

A shekarar 2022, Michael wanda ya daɗe yana jinya, ya samu taimakon kuɗi na Naira miliyan 5 daga Fasto Jeremiah Fufeyin domin kula da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Isra'ila za ta ji haushi, Najeriya ta saki shugaban Falasdinawa bayan kama shi

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa bayan ya samu sauki da farko, daga baya kuma lafiyarsa ta ƙara taɓarɓarewa.

Jarumi Duro.
Hoton Jarumi Michael da ya rasu bayan fama da jinya. Hoto: Stanley Ontop
Source: Instagram

Haka kuma a shekarar 2024, ya nemi taimakon kuɗi daga masu shirya fina-finai tare da roƙon a ƙara ba shi damar fitowa a fina-finai domin ya kula da kansa.

Marigayi Michael ya fito a cikin fitattun fina-finan masana'antar Nollywood da dama ciki har da Midnight Love (2003) da The Guilty (2006).

Jarumin Nollywood, Cif Kanran ya mutu

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood , Olusegun Akinremi, wanda aka fi sani da Cif Kanran, ya riga mu gidan gaskiya.

Cif Kanran sananne ne a masana’antar fina-finan Yarbawa saboda salon sa na musamman, kwarjini, son jin daɗi, barkwanci, da kuma kwarewa a sana'ar fim.

A tsawon shekarun da ya yi a Nollywood, ya fito a cikin fina-finai da dama irin su Ewe Orun, Aiye, Efunsetan Aniwura, Agbarin, da Bata Wahala.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262