Aure Ya Kawo Karuwa a Musulunci, An Ji Yadda Fitacciyar Jarumar Fim a Najeriya Ta Musulunta
- Jaruma Debbie Shokoya ta bayyana yadda ta musulunta bayan ta yi aure duk da cewa an haife ta a cikin addinin kirista
- Fitacciyar jarumar ta ce tun asali, ba ta taba raina wani addini ba kuma tana lokarin kyautata alakarta da Allah
- Ta kuma ja hankalin mutane kan zama da kowa lafiya da mutunta juna, tana mai jaddada muhimmancin mu'amala da mutane
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya kuma furodusa, Debbie Shokoya, ta yi karin haske kan yadda ta karbi addinin musulunci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jarumar ta shiga musulunci ne bayan ta yi aure, lamarin da masoyanta musamman musulmi suka yi farin ciki da shi.

Source: Instagram
Jarumar fina-finai ta musulunta bayan aure
Jaruma Debbie Shokoya ta bayyana abin da ya ja ra'ayinta har ta canza addini daga kiristanci zuwa addinin musulunci a shafinta na Istagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta sake jaddada cewa an haife ta a cikin addinin Kirista, amma daga baya ta fahimci gaskiya, ta karbi addinin musulunci bayan ta yi aure.
Debbie ta ce matakin da ta dauka ya ta’allaka ne kan alakarta ta kai tsaye da Allah, tare da jaddada muhimmancin soyayya, jin kai da tausayi a cikin mu’amala da mutane.
Yadda jaruma Debbie ke girmama addinai
A cewarta, bai kamata addini ya zama wani abu da zai haddasa rikici ko gasa ba, illa dai hanya ce ta rayuwa wadda ta ginu a kan zaman lafiya da soyayya.
Jarumar ta kuma jaddada cewa ba ta taba nuna bambanci tsakanin addinai ko kiyayya ga wani adddin ba.
Ta bayyana cewa a tsawon rayuwarta, ta fi maida hankali wajen ibadarta da ke sa ta jin daɗi da farin ciki a zuciya da yadda take kusantar Allah.
Cikakken jawabin sa jarumar ta yi
Debbie ta bayyana cewa:
“An haife ni a matsayin Kirista, amma na zama Musulma ta hanyar aure. Komai na Allah ne, ka kasance mai mutunta kowa. Ban taba nuna wariya ga kowanne addini ba.
"Mutunci ya kamata ya zo a farko idan ana magana kan addini. Ina gana wa da Allah ta hanyar da zuciyata ke samun natsuwa, domin abin da ya fi muhimmanci shi ne dangantakata da Allah da yadda nake mu’amala da mutane.
“Ba yaƙi ba ne, ba gasa ba ce, kuma ba muhawara ba ce. Ku yada soyayya kuma ku nuna wa kowa soyayya ba tare da la’akari da addini, ko launin fata, ko kabilar mutum ba, soyayya ita ce a farko saboda Allah Shi ke da soyayya.”

Source: Instagram
Mawaki ya ja ra'ayin matarsa ta musulunta
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen mawakin nan da ake danganta wa da ƙasashe biyu, Najeriya da Tanzania, Juma Jux ya musuluntar da matarsa.
Juma Jux, ya ce matarsa, Priscilla Ojo, ta musulunta tun kafin shagulgulan bikin aurensu da aka yi a watan Afrilu a jihar Legas.
Mawakin ya faɗi ƙalubalen da ya fuskanta wajen fahimtar da Priscilla addinin musulunci kafin ta musulunta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

