Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya Ya Saki Bidiyo ana tsaka da Jita Jitar Cewa Ya Mutu
- A baya-bayan nan aka fara yada jita-jitar cewa fitaccen jarumin Nollywood, Chiwetalu Agu ya mutu bayan fama da rashin lafiya
- Jarumi Agu ya saki faifan bidiyo a shafinsa na kafar sada zumunta, inda ya karyata labarin cewa ya rasu
- Ya bukaci yan uwa da masoyansa su yi watsi da wannan mummunan labari, yana mai cewa yana nan a raye kuma ba yanzu zai mutu ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Shahararren ɗan wasan Nollywood, Chiwetalu Agu, ya fito fili ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya rasu, inda ya bayyana labarin a matsayin karya.
Jarumin masana'antar shirya fina-finan ya roki daukacin masoyansa da yan uwa da abokan arziki su yi watsi da labarin mutuwarsa domin ba gakiya ba ne.

Source: Instagram
Jarumin Nollywood ya karyata labarin mutuwarsa
Chiwetalu Agu ya tabbatar da cewa yana nan bai mutu ba a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Instagram a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rubutun da ya haɗa da bidiyon, Jarumi Agu ya ce:
“Masoyana da yan uwa, ku yi watsi da duk wata jita-jitar mutuwata, ku kai rahoto shafin ɗan jaridar yanar gizon da ya fara yaɗa wannan ƙarya. Ina nan da rai da yardar Allah.”
Jarumi Agu ya ce yana da sauran kwanaki
A cikin bidiyon, Agu ya ƙara da ikirarin cewa ba yanzu zai mutu, kuma sai ya ga gawarwakin makiyan da ke yada mutuwarsa tun kafin lokacinsa ya yi.
“Ni, Cif Chiwetalu Agu ba zan mutu yanzu ba. A maimakon haka, ni ne zan birne maƙiya na. Wanda ya haƙa rami shi zai faɗa ciki. Wanda ya haƙa kabari shi zai faɗa ciki.
"Ban gama wasa da jikokina ba, kuma sai na ɗauke su na yi wasa da su cikin ƙoshin lafiya," in ji shi.
Fitaccen jarumin ya ƙara da cewa, da a ce ɗaya daga cikin manyan ’yan jarida ne ya wallafa labarin mutuwarsa, da ya shigar da ƙara a kotu kan bata suna.
Amma ya ce ya yi shiru ne saboda wanda ya yaɗa jita-jitar “har yanzu yana ta fama, yana son samun mabiya.”

Source: Instagram
Chiwetalu Agu ya aika sako ga masoyansa
Fitaccen ɗan wasan kwaikwayon ya nuna takaicinsa kan yadda mutane ke saurin yarda da labaran da ba a tabbatar ba, za a samu rahoton a Tribune Nigeria.
Jarumin ya ce:
“Abin mamaki shi ne, a wannan ƙarni na 21, akwai mutane da ke da saurin yarda da irin waɗannan labarai ba tare da sun tantance gaskiya ba.
"Ina rokon masoya da yan uwana, ku yi watsi da duk wata jita-jita, ku kuma tsawatar wa duk wanda ke yaɗa wannan mummunan labari kaina."
Jarumi Fabian Adibie ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa shahararren ɗan wasan a masana'antar Nollywood , Fabian Adibie ya rasu yana da shekara 82 a duniya.
Rahotanni daga makusantansa sun nuna cewa marigayin ya yi bankwana da duniya ne bayan fama da jinya ta tsawon lokaci, amma ba a fadi cutar da ta yi ajalinsa ba.
Mutuwar dattijon ta yi matukar taba mutane da dama musamman abokan aikinsa a masana'antar Nollywood duba da irin girman da yake da shi a idonsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


