Bayan Shan Suka, Gwamna Buni Ya Magantu kan Malam Nata'ala, Ya Ɗauki Alkawari

Bayan Shan Suka, Gwamna Buni Ya Magantu kan Malam Nata'ala, Ya Ɗauki Alkawari

  • An yi ta sukar gwamnatin jihar Yobe game da rashin lafiyar dan wasan Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata'ala
  • Daga bisani gwamnatin Yobe ta yi duba kan lamarin jarumin inda ta shirya taimaka masa saboda halin da ya shiga na jinya mai tsanani
  • Kwamishinan lafiya, Dakta Muhammad Lawan Gana, ya ce gwamnati za ta haɗa kai da asibitin domin tabbatar da ba shi kulawa ta musamman

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Gwamnatin Jihar Yobe ta yi magana kan rashin lafiyar da jarumin Kannywood ke fama da ita.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta amince za ta ɗauki dawainiyar dukkan kuɗaɗen jinyar Mato Yakubu.

Gwamnatin Mala Buni za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata'ala
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni yayin taro a Damaturu. Hoto: Yobe State Government.
Source: Facebook

Kwamishinan lafiya, Dakta Muhammad Lawan Gana shi ya bayyana haka lokacin da ya kai wa jarumin ziyara a gidansa da ke garin Potiskum, cewar Aminiya.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

Kyautar da gwamnatin Nijar ta ba Malam Nata'ala

A farkon makon nan, Malam Nata’ala ya bayyana cewa shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya taimaka masa da kuɗi naira miliyan 27.

Ya ce taimakon ya zo bayan ya roki jama’ar gari taimako don ci gaba da neman magani kan ciwon daji da yake fama da shi.

Wannan matakin ya sake bayyana yadda jarumin ke samun goyon baya daga gwamnati da shugabanni, domin ci gaba da rayuwa da kuma jinyarsa.

Lamarin ya jawo suka ga gwamnatin Yobe da ma na Najeriya duba da halin da jarumin ya shiga na matsanancin rashin lafiya wanda har sai da gwamnatin Nijar ta tallafa da miliyoyi.

Nata'ala ya soki Gwamna Buni da Nijar ta ba shi kyautar kudi
Gwamna Mai Mala Buni da Janar Abdourahamane Tchiani da Jarumi Mato Yakubu. Hoto: Gimbiyar Hausa, Mahaluki Nata'ala Potiskum.
Source: Facebook

Alkawarin da gwamnatin Yobe ta yi wa Nata'ala

Kwamishinan lafiya a Yobe ya bayyana cewa gwamnati za ta yi haɗin gwiwa da asibitin da yake jinya domin tabbatar da samun kulawa ta musamman.

Kara karanta wannan

An fasa ƙwai: Hon. Jibrin ya fallasa waɗanda ba su son Kwankwaso ya shiga APC

Ya ƙara da cewa wannan mataki yana nuna yadda Gwamna Buni ke tausaya wa jama’a tare da taimaka wa masu buƙatar kulawa.

Ya ce kuma hakan shaida ce ta jajircewar gwamnatin wajen inganta harkokin lafiya da samar da tallafi ga waɗanda ke cikin buƙata.

Abin da Nata'ala ya ce ga Gwamna Buni

Malam Nata’ala ya yi wa Gwamna Buni godiya bisa wannan alheri, yana mai cewa taimakon zai tallafa masa da iyalinsa wanda ba zai manta ba.

Ya yi addu’ar Allah ya saka da alheri ga gwamnan, tare da ci gaba da kare shi a dukkan al’amuran mulki da rayuwa saboda abin alheri da ya yi masa.

Malam Nata'ala ya roki taimakon al'umma

Mun ba ku labarin cewa fitaccen dan wasan Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata’ala ya bayyana mawuyacin hali da yake ciki.

Malam Nata’ala ya tabbatar da cewa yana fama da cutar daji, inda ya bayyana bukatar taimakon addu’o’in al'umma da kudi.

Jarumin ya godewa masu taimaka masa ciki har da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malaman addini da masana’antar Kannywood.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.