"Har da Babana," Jarumar Fim Ta Rikita Intanet, Ta Ce Mazan Najeriya Maciya Amana ne

"Har da Babana," Jarumar Fim Ta Rikita Intanet, Ta Ce Mazan Najeriya Maciya Amana ne

  • Jaruma Bimbo Akintola ta caccaki mazan Najeriya, tana mai cewa kashi 99 cikin 100 duk su na cin manar matansu
  • Fitacciyar jarumar fina-finan ta ce al'adu kamar na auren mata fiye da daya na taimaka wa wajen cin amanar da maza ke yi a yanzu
  • Ta bukaci yan uwanta mata su fuskanci gaskiya a zahiri, su daina rabuwa da samari ko mazansu saboda sun ci amanarsu domin abin a jininsu yake

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Fitacciyar ‘yar fim ta Najeriya, Bimbo Akintola, ta tayar da kura a shafukan sada zumunta bayan ta bayyana cewa cin amana a wurin maza ya zama ruwan dare.

Jarumar fina-finan Najeriya ta yi ikirarin cewa kusan kashi 90 zuwa 99 na mazan kasar nan ba su da amanar zama da mace daya.

Kara karanta wannan

Da gaske an yi wa Sheikh Jingir ihu a Abuja? Izala ta fadi abin da ya faru

Jaruma Bimbo Akintola.
Hotunan jarumar fima a Najeriya, Bimbo Akintola Hoto: Bimbo Akintola
Source: Instagram

A rahoton da The Nation ta tattaro, Bimbo Akintola ta ce hakan ya na da alaka da al’adun kara aure da kuma tarbiyyar da galibin mazan suka samu daga iyayensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaruma ta zargi mazan Najeriya da cin amana

A wata hira da aka yi da ita kwanan nan, Jaruma Bimbo Akintola ta ce,

“Yawancin mazajenmu su na cin amanar mu. Ka kalli gidan ku, mahaifinka ya na cin amana, kakanka ma ya yi cin amanar nan amma ku yi hakuri, gaskiya ce.
"Aure mace fiye da ɗaya, kara aure, ko kunya ba su ji. Mahaifina ma yana da mata biyu. Ban san daga ina aka kawo maganar zama da mace ɗaya a Afrika ba tun farko.
"Gaskiyar magana ita ce, kashi 90 zuwa 99 na maza suna cin amanar matansu. Wannan abu a jinin su yake, wasu ma suna tasowa su biyo halin mahaifansu na zuwa ganin budurwa a boye.”

Kara karanta wannan

ADC: An samu wanda zai dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a 2027

Bimbo Akintola ta kara da cewa wasu maza suna tasowa suna koyo daga iyayensu maza, har ma suna bin su wajen ziyartar budurwansu.

Jaruma Bimbo Akintola ta ba mata shawara

Ta kuma kawo misali da shahararrun ma’aurata irin su Beyoncé da Jay-Z, inda ta ce, “Kin rabu da wani namiji saboda ya ci amanar ki, kin koma ga wani, matsalar iri ɗaya ce duk halinsu daya.

"Jay-Z ya ci amanar Beyoncé, ta bar shi? A’a. Don haka mu fuskanci gaskiya, maza duk halinsu daya," in ji ta.
Jaruma Bimbo Akintola.
Hotunan jarumar fim a Najeriya, Bimbo Akintola Hoto: Bimbo Akintola
Source: Instagram

Wannan magana ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu suka amince da ra’ayin jarumar cewa wasu al’adu na taka rawa wajen bai wa maza damar cin amana.

Sai dai wasu da dama sun caccake ta, suna ganin tana ƙarfafa cin amana maimakon ta yi Allah-wadai da shi, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Auren jarumar fim a Najeriya ya mutu

A wani rahoton, kun ji cewa jaruma Abiola Adebayo ta tabbatar wa duniya cewa aure ya kare tsakaninta da mijinta Oluwaseyi Akinrinde tun shekarar 2024 da ta gabata.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

Wannan kalamai da fitacciyar jarumar ta masana'antar shirya fina-finan Nollywood din ta yi ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa kan mutuwar aurenta.

Jarumar ta bayyana wa mutane cewa ta shafe watanni 14 tana zubar da hawaye a kusan kowanne dare tun bayan mutuwar aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262