Nata'ala: Jarumin Kannywood Ya Roki Taimako bayan Faɗin Halin da Yake ciki

Nata'ala: Jarumin Kannywood Ya Roki Taimako bayan Faɗin Halin da Yake ciki

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata’ala ya bayyana mawuyacin hali da yake ciki
  • Malam Nata’ala ya tabbatar da cewa yana fama da cutar daji, inda ya bayyana bukatar taimakon addu’o’in al'umma da kudi
  • Jarumin ya godewa masu taimaka masa ciki har da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malaman addini da masana’antar Kannywood

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Potiskum, Yobe - Jatumin Kannywood, Mato Yakubu ya fitar da wani bidiyo inda aka gano shi a cikin mawuyacin hali na jinya.

Fitaccen jarumin da aka fi sani da Malam Nata'ala a shirin Dadin Kowa ya tabbatar da cewa yana fama da jinya.

Malam Nata'ala ya nemi taimako saboda rashin lafiya
Malam Nata'ala lokacin da yake da lafiya da yanzu da yake fama da jinya. Hoto: Mahaluki Nata'ala Potiskum.
Source: Facebook

Halin da Malam Nata'ala yake ciki a yanzu

Nata'la ya bayyana haka ne a cikin wata hira da DCL Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook a yau Litinin.

Kara karanta wannan

Da gaske jarumi Ali Nuhu ya rasu? Shugaban NFC ya warware rudanin da aka samu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, Nata'ala ya ce tabbas ba shi da lafiya kuma babu karya a ciki yana fama da jinya inda ya roki taimako da addu'o'i har da kudi saboda a yanzu karfinsa ya kare.

Ya ce:

"Farko dai karin bayani da nake da shi faifan bidiyo da ke yawo fuskata ce ba wani ba, duk bayanin da na yi gaskiya ne, ba ni da lafiya.
"Ina bukatar taimakon addu'a da kudi saboda jinya ce mai hatsari kuma karfi na ya gaza, duk sati uku zan yi allurar N250,000 har na wata shida, ban da magaunguna da kudin gado."
Malam Nata'ala ya fadi wadanda suka taimaka masa a jinya
Jarumin Kannywood, Malam Nata'ala yayin shirin fim a matsayin malamin zaure. Hoto: Mahaluki Nata'ala Potiskum.
Source: Facebook

Rokon Nata'ala ga al'umma game da jinyarsa

Jarumin ya ce yana neman taimako ga duk wanda Allah ya horewa saboda irin makudan kudi da yake kashewa kowane mako uku.

Ya kara da cewa:

"Duk wanda Allah ya ba shi ikon taimakamin ina bukata daga ma'aikatan gwamnati, jami'an tsaro, yan kasuwa, kungiyoyin farar hula ko sarakunanmu na gargajiya.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta kara taba 'yan fim a Najeriya, fitaccen jarumi ya riga mu gidan gaskiya

"Mutane za su ga na rame kamar na fito daga shirya fim na 'horror', akwai wata cuta da ake kira daji ita ce ke damu na a yanzu."

Nata'ala ya godewa al'umma game da taimakonsu

Nata'ala ya ce tabbas an ba shi taimako daidai gwargwado kuma ya bayyana wadanda suka tallafa masa tun fara jinyarsa ciki har da masana'antar Kannywood.

"Mutane da yawa sun kawo mani taimako wanda ba zai kirgu ba, akwai malaman addini ta kowane bangare sun taimaka da addu'o'i''.
"Sannan yan kasuwarmu da yan siyasa da kungiyoyin fararen hula sun tura mani gudunmawa.
"Masana'antar Kannywood ta aika mani da gudunmawa haka tashar Arewa24 ta ba ni gudunmawa da sauran jama'a da dama."

- Cewar Jarumi Nata'ala

Daga karshe jarumin ya yi addu'a ga wandada suka taimaka masa ta kowane bangare yayin jinyar yake yi.

Ya roki Allah ya ba masu jinya lafiya sannan ya roki Ubangiji ya tashi kafadunsa idan na sauki ne idan kuma na tafiya ne Allah ya ba shi sa'ar tafiya.

Malam Nata'ala ya nisanta kansa da yabon Buhari

A wani labarin, jarumi Mato Yakubu, wanda aka fi sani da sunan Malam Nata'ala ya nesanta kansa da bidiyon da ke yawo na yabon Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Ya sanar da cewa, a baya shi 'dan gani-kashenin shugaban kasar a lokacin mulkinsa amma daga baya sun yi hannun riga da shi.

Ya ce rashin tsaro, matsin rayuwa da watsi da aka yi da su duka da kokarin da suka yi na kafa gwamnatin yasa ya dawo daga rakiyar Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.