Mutuwa Ta Kara Taba 'Yan Fim a Najeriya, Fitaccen Jarumi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Ta Kara Taba 'Yan Fim a Najeriya, Fitaccen Jarumi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jarumin masana'antar shirya fina-finan Nollywood, Olusegun Akinremi da aka fi sani da Cif Kanran ya mutu yana da shekaru 70 a duniya
  • An tabbatar da cewa jarumin wanda ya shahara wajen fitowa a matsayin sarki ko mai mulki ya rasu ne da safiyar yau Juma'a
  • A shekarun baya, Cif Kanran ya bayyana cewa ya ja baya dad'ga ashiga harkar shirin fina-finai saboda wasu matsaloli da yake fuskanta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Olusegun Akinremi, wanda aka fi sani da Cif Kanran, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 70.

Rahotanni daga abokan aikinsa a masana'antar shirya fina-finan kudancin Najeriya sun nuna cewa ya mutu ne da safiyar yau Juma'a.

Marigayi Jarumi Cif Kanran.
Hoton marigayi fitaccen jarumin Nollywood, Cif Kanran a tsaye a kofar gida lokacin da yake raye Hoto: @WavesNG
Asali: Twitter

Jarumin Nollywood, Cif Kanran ya rasu

Mai shairya fina-finai, Seun Oloketuyi, ne ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a, 15 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta cewa:

“Fitaccen jarumi. Segun Remi wanda aka fi sani da Cif Kanran ya rasu da safiyar Juma’a. Za a bayyana cikakkun bayanai daga baya.”

Cif Kanran sananne ne a masana’antar fina-finan Yarbawa saboda salon sa na musamman, kwarjini, son jin daɗi, barkwanci, da kuma gwaninta da basirar da yake da ita.

Yadda ya ja baya daga shiga fim kafin rasuwa

A wata hira da jaridar Punch ta yi da shi a shekarar 2020, jarumin ya bayyana wasu matsalolin da yake fuskanta, wadanda suka sa ya ja baya daga harkar fim.

“Na ja baya daga harkar fim saboda wasu dalilai. Siyasa ta shiga ko ina, akwai ƙungiyoyi daban-daban har ma a sana’armu.
"Wasu a masana’antar suna ganin mutane kamar ni a matsayin barazana saboda bana yin abin da bai dace ba a fannin sana’a, kuma hakan ya sa wasu ke jin haushi na," in ji shi.

Takaitaccen bayani kan Marigayi Cif Kanran

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

Ya fara harkar fina-finai ne a dandalin wasan kwaikwayo kafin ya koma talabijin da fim, inda ya fito a cikin dama-dama daga cikin fitattun wasannin kwaikwayo na Yarbawa.

Marigayi Cif Kanran ya yi fice a wani shahararren fin da aka rika nunawa a NTA. Shahararsa ta ƙara bunƙasa bayan fitowa a fina-finan Yarbawa.

A tsawon shekarun da ya yi a Nollywood, ya fito a cikin fina-finai da dama irin su Ewe Orun, Aiye, Efunsetan Aniwura, Agbarin, da Bata Wahala.

Jarumin ya fi yawan fitowa a matsayin mai mulki, sarki, ko dattijo a fina-finai. A halin yanzu, ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba.

Jarumar Nollywood, Omotola ta mutu

A wani labarin, kun ji cewa fitacciyar jarumar Nollywood da ke tashe, Omotola Odunsi ta riga mu gidan gaskiya ranar Alhamis.

Fitaccen jarumi Odunlade Adekola, wanda ya horar da ita a masana'antar fina-finai, ya tabbatar da rasuwarta tare da alhinin wannan babban rashi da suka yi.

Omotola ta fara aiki a matsayin jami’ar kula da harkokin bashi a wani banki kafin ta yi murabus a shekarar 2019 domin bin burinta na yin fim.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262