Rahama Sadau Ta Maida Martani ga Sakon Wani Masoyinta Kwanaki 2 bayan Ta Yi Aure

Rahama Sadau Ta Maida Martani ga Sakon Wani Masoyinta Kwanaki 2 bayan Ta Yi Aure

  • Jarumar Kannyood da ta yi aure a karshen makon da ya gabata, Rahama Sadau ta fara amsa sakonnin da masoya ke tura mata na fatan alheri
  • Tun bayan samun labarin daura aurenta, jarumai daga Kannywood da masoyan Rahama suka fara tofa albarkacin bakinau tare da mata fatan alheri
  • Rahama Sadau ta ji dadin sakon da wani masoyinta ya tura mata, inda ta amsa masa tare da godiya bisa addu'o'in da ya kwarara mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - A ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025, aka daura auren fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau a jihar Kaduna.

Rahama wanda ta shahara a fannin fina-finan Hausa da na turanci ta auri wani mai suna Ibrahim Garba bisa sadaki a N300,000.

Jarumar Kannywood, Rahama Sadau.
Rahama Sadau ta ji dadin sakon fatan alheri da wani masoyinta ya tura mata Hoto: Rahama Sadau
Asali: Instagram

A wani sako da ta wallafa a shafin X, Rahama Sadau ta roki yan uwan da abokan arziki da kuma masoyansa su sanya ta a addu'a, Allah Ya ba su zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Auren Rahama Sadau ya ja hankalin jama'a

Bikin jarumar dai ya ja hankalin mabiyan harkokin Kannywood a Arewacin Najeriya musamman ganin yadda aka daura auren ba tare da sanarwa ba.

Dan uwan Rahama Sadau, Haruna Ibrahim, wanda aka fi sani da Abba Sadau, ya ce sun shirya bikin ne cikin sirri har sai ranar daura aure, sannan mutane suka sani.

Tun bayan daura auren, yan uwa da abokan arziki suka fara tura sakon addu'a da fatan alheri ga Rahama Sadau.

Jarumai a Kannywood, kamar Ali Nuhu, Ali Jita, Adam A.Zango, Umar M. Shareef da sauran abokan aiki sun taya Rahama murna tare da fatan Allah sa gidan zamanta ne.

Masoyin Rahama Sadau ya tura mata sako

Wani mai amfani da shafin X, Sarki ya wallafa sakon murna da fatan Allah Ya sa albarka a auren jaruma Rahama Sadau a shafinsa tun a ranar da aka daura aure.

Kara karanta wannan

Bayan Adamawa, NiMet ta ce jihohin Arewa 2 za su fuskanci ambaliya ranar Talata

A sakon, Sarki ya ce:

"Ina taya ki murna, Rahma Sadau, Allah ya albarkaci auranku, Ya cika shi da soyayya, jin ƙai da fahimtar juna, Ya kuma sanya shi ya zama mabudin alheri a gare ku a rayuwar duniya da kuma tushen lada madawwami a lahira."
Rahama Sadau.
Rahama Sadau ta amsa sakon fatan alheri bayan ta yi aure Hoto: Rahama Sadau
Asali: Instagram

Amsar da Rahama Sadau ta tura masa

Kwanaki biyu bayan haka, a yau Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025, Rahama Sadau ta maida martani ga wannan sako tare da godiya da wannan addu'a da masoyin nata ya yi mata.

"Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum, ina godiya matuka da wannan addu'a da fatan alheri da ka yi mani," in ji Rahama Sadau.

Sakon Rahama Sadau bayan daura aurenta

A wani rahoton, kun ji cewa Rahama Sadau ta tabbatar da labarin da ke ta yawo cewa an ɗaura aurenta a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025 a Kaduna.

Jarumar bayyana farin cikinta da Allah ya nuna mata wannan rana da ta zama matar aure bayan bin duka matakan da adddinin Musulunci ya shar'anta.

Rahama Sadau ta roki a sanya ta a addu'a Allah ya dawwamar da soyayya a gidanta kuma Ya sa wa auren albarka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel