"Mutuwa Mai Yankar Kauna": Matashiyar Jarumar Fina Finai Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finai watau Nollywood, Pat Uguwu ta mutu tana da shekara 35 a duniya
- Abokin aikinta a masana'antar, Jarumi Emeka Okoye ne ya sanar da rasuwar matashiyar a shafinsa yau Laraba, 5 ga watan Janairu, 2025
- Tuni dai jarumai mata da maza daga Nollywood suka fara tura sakon ta'aziyya da alhinin mutuwar Pat Ugwu tare da yi mata addu'a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood da ke kudancin Najeriya ta shiga jimami yayin da aka sanar da mutuwar matashiyar jaruma, Pat Ugwu.
Fitacciyar jarumar Nollywood, Pat Ugwu ta riga mu gidan gaskiya tana da shekara 35 a duniya.

Asali: Instagram
Matashiyar jarumar Nollywood ta mutu
Wani abokin aikinta, Emeka Okoye, ne ya sanar da mutuwarta a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okoye ya kuma wallafa takardar tsare-tsaren jana’izarta da ke bayyana yadda za a birne marigayiyar.
Pat Ugwu ta rasa mahaifinta a shekarar 2021, kuma za a yi jana’izarta a ranar 7 ga Fabrairu, 2025.
Emeka Okoye ya nuna alhininsa bisa wannna rashi da suka yi a Nollywood tare da addu'ar Allah ya sa da samu salama.
"Ki huta lafiya, ‘yar uwa. @patpat_ugwu, kenan ba za mu ƙara yin aiki tare ba? Mutuwa ta mana yankan ƙauna, don Allah Ki huta lafiya, Pat. Allah sa ki huta cikin rahamarsa.”
Jarumin ya kuma yi addu’a ga abokan aikinsa:
"Ya Allah, ka kare duk abokan aikina, musamman wadanda nake tare da su. Wannan yawaitar rasuwa tana da ban tsoro. Ina rokon rayuwa ga kowa a wannan shekara ta 2025, Amin."
Manyan jarumai sun miƙa sakon ta'aziyya
Wasu shahararrun jaruman masana'antar Nollywood sun nuna jimaminsu kan wannan rashi.
Destiny Etiko ta rubuta a shafin ta: “Yesu, a’a!!!”
Kevin Mike ya ce:
“Na tashi da safe kawai na ji labarin mutuwar daya daga cikin ‘yan uwana a masana’antar mu, Pat Ugwu. Ki huta lafiya, masoyiya.”
Haka nan, Rita Edochie, Nkechi Blessing, da wasu da dama sun yi alhini da mutuwar Pat Ugwu.
Ana sa ran jana’izarta za ta tara ‘yan fim da masoyanta domin karramata tare da yi mata addu’a.
Fitaccen jarumin Nollywood ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa jarumin fim da ya daɗe ana gogawa da shi a Nollywood, Pa Charles Olumo Sanyaolu ya mutu yana da shekaru 101.
A ruwaito cewa marigayin ya rasu ne lokacin da ya koma barci bayan ya yi ƙorafin cewa yana jin gajiya a tattare da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng