"Ba Dole sai Saurayinki ba": Hadiza Gabon Ta ba Ƴan Mata Shawarar Wanda Za Su Aura

"Ba Dole sai Saurayinki ba": Hadiza Gabon Ta ba Ƴan Mata Shawarar Wanda Za Su Aura

  • Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta ba 'yan mata shawara, tana cewa ba dole sai samarinsu ba, ko mijin wata za su iya aura
  • Hadiza Gabon ta ce sakon shawararta ya fito ne daga daraktan finafinai, Hassan Giggs, wanda ya ja hankalin mata a soshiyal midiya
  • Sama da mutane 7,500 ne suka nuna goyon baya ga sakon jarumar, yayin da masu tsokaci suka samu sabanin kan wannan shawarar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - An samu sabon darasin da ake tattauna a kan shi yanzu a soshiyal midiya yayin da jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta yi magana kan aure.

Hadiza Gabon, wacce ta sha samun tambayoyi kan "yaushe za ki yi aure" ta fito ta ba 'yan mata shawarar kalar mazan da ya kamata su aura.

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

Hadiza Gabon ta yi magana kan mazan da ya kamata 'yan mata su mayar da hankali wajen aure
Hadiza Gabon ta ba 'yan mata shawarar auren mazajen aure maimakon jiran samarinsu. Hoto: adizatou
Asali: Instagram

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Alhamis, fitacciyar 'yar wasan ta ce 'yan mata su daina damuwa lallai sai sun auri samarinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadiza Gabon ta ba 'yan mata shawara

Jaruma Hadiza Gabon ta nuna alamar cewa yanzu lokaci ya wuce da 'yan mata da za su nace akan sai sun auri saurayin da suke soyayya da shi.

Game da wanda ya kamata mata su aura, 'yar wasar ta ce "ko mijin wata kika samu ki aura" wanda ke nuna girman shawararta ga 'yan matan.

A cewar Gabon:

"Ba dole sai saurayinki ba, ko mijin wata kika samu ki aura."

Amma ta ce daraktan finafinan Hausa, Hassan Giggs ne ya tura mata wannan sakon domin ta wallafa a shafinta na Instagram.

Mutane sun yi tsokaci kan shawarar Gabon

Sama da mutane 7,500 ne suka nuna alamar sun ji dadin wannan sako na jarumar yayin da sama da mutane 450 suka yi tsokaci a kai.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin masu bibiyar jarumar:

jiddarh_caps:

"Wata ta aure min sarauyi babu kunya bare tsoran Allah, nima mijin wata zan aura kowa yaji babu dadi."

shamciyer:

"A to, gaya masu dai 'yar uwa, mu dama mijin wata shi ne burin mu."

harunmahammadt:

"Allah ya kai haske kabarin El Mu'az, in dai naga kin dora wani abu na dariya shi kawai nake tunawa, Allah ya sa mu hadu a Alannah."

___hafsatuu:

"Ko baban saurayin naki kIka samu ki aure."

haleemaah__:

"Wai mijin wata, ku ce mai mata kawai, kuma kaddara ai duk wanda Allah yasa za ka aura shi ne mijinka, ba ja da baya ko saurayin ko mai matar. Allah dai ya ba mu nagarin."

fatima_ummu:

"To mata ku kula da mazajenku, dije ta na fatawa, kar kuma a yi korafi a baya."

incense.by.sadeeya:

"Ai ni hankali na ya fi kwanciya da mai matar ma, kuma ko za su mutu sai mun shiga."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza fada da 'yan ta'adda a jihohi, sun kwato makamai

Idan Hadiza ta shirya zan iya aurenta

Wani matashi a anguwar Makarfi, da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Mubarak Kamal Player, ya ce shi zai iya auren Hadiza Gabon idan har za ta ba shi dama.

Mubarak Kamal ya ce yana jin takaici yadda za a ce "kyakkyawar mace mai sura" irin Hadiza Gabon ace har yanzu ba ta yi aure ba, alhalin ya san tana da masoya.

Matashin ya ce:

"Ina da sana'ata, kuma ina crypto, ka ga zan iya kula da ita daidai gwargwado. Idan har za ta amince, to ni zan iya aurenta."

Matashin ya ce ya yi wannan maganar ne saboda tsananin kaunar da yake yiwa jarumar, yana mai cewa "duk cikin matan Kannywood, Hadiza ce kawai nake kauna."

Hadiza Gabon ta sha kalaman yabo

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hassan Giggs ya yaba wa Hadiza Gabon kan alherin da ta rika yi masa, yana mai cewa tana matukar daraja shi da iyalinsa.

Daraktan fina finan na Hausa ya ce Hadiza Gabon na a sahun gaba a jaruman da yake mutuntawa a masana'antar Kannywood.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.