Hassan Giggs Ya Fadi Sunan Jarumar Kannywood da Ta Yi Masa Babban Alheri a 2024

Hassan Giggs Ya Fadi Sunan Jarumar Kannywood da Ta Yi Masa Babban Alheri a 2024

  • Hassan Giggs ya yaba wa Hadiza Gabon kan alherin da ta rika yi masa, yana mai cewa tana matukar daraja shi da iyalinsa
  • Daraktan fina finan na Hausa ya ce Hadiza Gabon na a sahun gaba a jaruman da yake mutuntawa a masana'antar Kannywood
  • A wani sakon godiya da ya wallafa a shafukansa na soshiyal midiya, Hassan Giggs ya fadi alherin da Gabon ta yi masa a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitaccen darakta (mai ba da umarni) a masana'antar Kannywood, Hassan Giggs ya yi ruwan kalaman yabo ga shahararriyar 'yar wasa, Hadiza Gabon.

A yayin da shekarar 2024 ta zo karshe, darakta Hassan Giggs ya tuno da irin abubuwan alherin da jaruma Hadiza Gabon ta yi masa daga Janairu zuwa Disamba.

Hassan Giggs ya yi magana kan abubuwan alherin da jaruma Hadiza Gabon ta yi masa
Hassan Giggs ya rubuta sakon godiya ga jaruma Hadiza Gabon yayin da 2024 ta kare. Hoto: adizatou
Asali: Instagram

A wani sakon godiya da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Hassan Giggs ya ce Hadiza Gabon na sahun gaba a jaruman da yake girmama su a Kannywood.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a jihar Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alherin Hadiza Gabon ga Hassan Giggs

Mai ba da umarni a fina finan Hausa ya ce akwai lokuta da dama da Hadiza Gabon ke yi masa kyauta ta ban mamaki, musamman idan aiki ya hada su.

Hassan Giggs ya ce tun da ya ke da Hadiza Gabon, ciniki bai taba hada su idan aka zo aiki ba, kawai sai dai ya ji ruwan kudi a asusunsa.

Alherin Hadiza Gabon bai tsaya ga kudi kawai ba, inda darakta Hassan Giggs ya ce jarumar Kannywood din ta na matukar kauna da mutunta iyalinsa.

Sakon godiyar Hassan Giggs ga Gabon

Sakon godiya da Hassan Giggs ya rubutawa Hadiza Gabon na cewa:

"Godiya Dije @adizatou kamar yadda na saba kiranta, daya daga cikin jaruman da nake girmama su a masana'antar Kannywood.
"Ba zan manta da abin alheri da ki ka yi mani ba, ta wajen ayyukan da muka yi da ke, ciniki bai taba hadani da ke ba sai da naji wani 'alert' mai fasa waya.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisa ya fadi abin da ya faru kan kwace filinsa, ya gargadi hukumar FCTA

"Ta na girmama ni sosai, tana kaunar iyalina, za ki gama da duniya lafiya inshaa ALLAH.
"Amma ba zan manta da jirgin da na rasa daga Abuja zuwa Kano ba, sai karfe 5 na Asuba jirgi ya zo kamar mun tafi Umara. Na gode da tunawar da kike da ni idan abin alkhairi ya taso."

Hadiza Gabon ta tuna da marigayi El-Muaz

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitacciyar 'yar wasan Kannywood, Hadiza Gabon ta wallafa bidiyon da ta yi da marigayi El-Muaz Birnawa lokacin da suke wasa da dariya.

Hadiza Gabon ta yi kalamai masu ratsa zuciya wadanda ke nuna tsantsar damuwar da take ciki game da mutuwar mawaki El-Muaz, dan asalin jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.