Mawaki Rarara Ya Rikita Midiya, Ya Saki Sabuwar Wakar da Ta Jefa Mutane a Mamaki

Mawaki Rarara Ya Rikita Midiya, Ya Saki Sabuwar Wakar da Ta Jefa Mutane a Mamaki

  • Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya sake tayar da kura a soshiyal midiya bayan ya saki wata sabuwar wakar biki mai ban sha'awa
  • Aisha Humaira ta wallafa bidiyon wakar da Rarara ya yiwa Alhaji Ibrahim da amaryarsa Khadija, wanda ya jawo martani sosai
  • Mawakin ya yi shigar kananan kaya a bidiyon, wanda ya kara jan hankalin masoya, yayin da mutane ke yaba wa sabuwar wakarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitaccen mawakin siyasar Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya sake rikita soshiyal midiya bayan ya saki wata zazzafar sabuwar waka.

Maimakon a ji mawakin ya fitar da wakar siyasa, sai kwatsam a ka ji shi dauke da wakar biki, wadda ya yiwa wani ango da amaryarsa.

Mawaki Rarara ya saki sabuwar wakar biki
Aisha Humaira ta fitar da gajeren bidiyon sabuwar wakar mawaki Rarara. Hoto: ayshatulhumairah
Asali: Instagram

Rarara ya saki sabuwar wakar biki

Ta hannun daman Dauda Rara, watau Aisha Humaira ce ta wallafa gajeren bidiyon wakar a shafinta na Instagram inda take sanar da cewa "wakar ta fita."

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki Ado Gwanja zai sake rikita Arewa, ya saki sabon kundin wakoki 18

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba wannan ne karon farko da mawakin ya sauka daga layin wakar siyasa ba, ko a baya anji shi ya na rera wakoki da suka shafi tsaro, zamantakewa da kuma soyayya.

Haka zalika, a kwanakin baya mawakin ya jawo ka-ce-na-ce bayan ya fitar da wata waka mai taken 'Fati Fatima Mai Zogale' wacce ya ce ta jawo masa karin masoya.

Rarara ya yi shigar kananan kaya

To a wannan karon dai, an ji mawakin ya saki sabuwar wakar biki wadda ya yiwa wani Alhaji Ibrahim Yakubu da amaryarsa Khadija.

A cikin bidiyon da Aisha Humaira ta saki, an ga jarumar tare da mawakin a cikin wani falo da ake kyautata zaton gidansa ne, tare da mai yi masa kida "Andus."

Mawaki Rarara na sanye da kananan kaya, riga da wanko da kuma madaurin wuya, inda ita Aisha Humaira ta sha kwalliya da leshi.

Mutane sun yi martani kan sabuwar wakar

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Wannan bidiyo da Aisha Humaira ta saki ya jawo ce-ce-ku-ce inda ma'abota soshiyal midiya ke cewa:

danlanso_gama:

"Masha Allahu ciyaman wannan shiga ta yi."

adam_m_ishaq_kano:

"Haka ake wakar aure dama."

dr.matazzz:

"Gaskiya ne wakar ta yi Allah ya kara basira."

itz_kastin_gee:

"Su Rarara kuma yanzu harka ta girmama… Na ga wannan 'tie' din."

mustapha.alawi.96:

"Wai ke mai ya sa Rarara ba zai aure ki ba ne. Ke ma ya ci a ce kin shiga daga ciki da wannan yawan amshin wakar naki ai."

auwalunaabba:

"Jami'ar waka, Allah ya kara basira."

Kalli bidiyon a nan kasa:

Mawaki ya biya sadakin Aisha Humaira?

A wani labarin, mun ruwaito cewa jaruma Aisha Humaira ta yi martani kan zarge zargen da ake yi na cewa mawaki Dauda Kahutu Rarara ya biya kudin sadakinta.

Jarumar Kannywood din ta shaida wa duniya cewa mawaki Rarara bai biya kudin sadakinta ba, kuma zancen za su yi aure ba gaskiya ba ne ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.