Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta saki zafafan hotunan ta tana busa sigari
- Jaruma Nafisa Abdullahi ta saki zafafan hotunan ta tana busa sigari
- Wannan hali dai bai yi wa da yawa daga masoyan ta dadi ba
- A kwanan baya jarumar at samu sa-in-sa da abokiyar sana'ar ta watau Rahma Sadau
A wani salo na fitsara da rashin tarbiyya, mun samu cewa fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta sa saki wasu hotuna da kuma gajejjerun faya-fayan bidiyoyin ta tana ta busar sigari.
KU KARANTA: Wasu bata-gari sun yi wa Aisha Tsamiya kutse
A cikin hotunan dai an ga jarumar tana ta zukar sigarin sannan kuma ta ta furzar da bakin hakin da ta zuka da bakin ta cikin annashuwa da kuma farin ciki.
Legit.ng ta samu cewa sai dai wannan hali da kuma dabi'ar da jarumar ta nuna ko kadan bai yi wa da yawa daga masoyan ta dadi ba inda suka yi ta yin tir da Allah-wadai da hakan tare kuma da bata shawarwari.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai jarumar sun dan samu sa-in-sa ta wata jarumar kuma abokiyar sana'ar ta a masana'antar watau Rahma Sadau kafin daga bisani su fito su karyata hakan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng