Jarumar Kannywood, Bilkisu Ta Saki Sababbin Hotuna da Suka Bayyana Surar Jikinta
- Jarumar Kannywood Bilkisu Salis ta gamu da fushin mutane kan shigar da ta yi a wasu sababbin hotuna da ta saki kwanan nan
- Masu bibiyar jaruma Bilkisu sun yi tsokaci iri-iri, wasu na yabawa kyawunta, yayin da wasu da dama ke caccakar shigar da ta yi
- Sama da mutane 1,100 sun nuna alamar kauna ga hotunan, yayin da wasu masu tsokaci ke jan hankalinta kan bin dokokin addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Wata 'yar wasar Kannywood, Bilkisu Salis, ta saki wasu sababbin zafafan hotuna a shafukan sada zumunta da suka jawo mata zagi.
Masoya da masu bibiyar jarumar a soshiyal midiya sun nuna matukar bacin ransu kan "mummunar" shigar da ta yi kuma ta wallafa a yanar gizo.
A ranar Juma'a, jaruma Bilkisu Salis ta wallafa hotunan da ake ta ka-ce-na-ce a kansu a shafinta na Instagram mai mabiya sama da 66,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da ta wallafa hotunan, 'yar wasar kwaikwayon ta yi addu'o'i da Larabci tana mai cewa:
"Ya Ubangiji ka sanya ni da zuriyata mu zamo masu tsayar da Sallah. Ya Ubangiji ka karɓi addu'ata.
"Ya Ubangiji ka gafarta mini, da iyayena da dukkan muminai a ranar da za a tsayar da hisabi."
Sama da mutane 1,100 suka nuna alamar 'kauna' a kan hotunan da ta wallafa, yayin da sama da mutane 50 suka tofa albarkacin bakinsu.
Mutane sun yiwa jaruma Bilkisu tatas
A yayin da wasu daga cikin masu tsokaci suka rika kuranta kyawun jarumar, wasu a hannu daya sun yiwa Bilkisu tatas kan irin shigar da ta yi.
Legit Hausa ta tattaro kadan daga ra'ayoyin masu bibiyar jarumar kan hotunan da ta wallafa:
realharunzender:
"Masha Allah, da kyau da kyau, fatan nasara jarumata."
huzzy_boy_:
"Wallahi a ji tsoron Allah."
dannazi014:
"Allah ya shirya ki, amma avacoin dinki duk a waje, wata rana uwa ce ke."
queen_fiddau13:
"Ba za dai ki bari ba, duk da wa'azantuwar da mutuwa ke mana."
real_sulee2000:
"Nonuwanki a waje, Allah ya kyauta."
shariff_mahmud_
"Ke da nake girmamawa za ki yi wannan shigar? Wallahi Annabi ya tsinewa wannan shigar."
realnasirabdullahi:
"kofar aljanna a bude take, kofar wuta ma a bude take sai wadda ka ga damar shiga."
abbasgas1:
"Kin yi kyau, amma gaskiya kin bar nonuwanki a waje."
saifullahisabowaizi:
"Bai dace da ke ba irin wannan shigar, haramun ne, ya kamata ki hankalta. Akwai mutuwa tana zuwa kowane lokaci."
Kalli hotunan jarumar da suka tayar da kura a kasa:
Hotuna: Jaruma Rayya ta jawowa kanta magana
A wani labarin, mun ruwaito cewa ma'abota soshiyal midiya sun yiwa jarumar Kannywood, Rayya Kwana Casa'in kaca kaca kan shigar da ta yi.
A wasu hotuna na murnar karin shekara da Rayya ta fitar, an ga jarumar ta yi shigar da ta nuna wasu sassan jikinta, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Asali: Legit.ng