'Akwai Ciwo': An Gano Bidiyon Hadiza Gabon da Marigayi El Muaz Suna Wasa da Dariya
- Hadiza Gabon ta tuna da marigayi El-Muaz Birniwa wanda ya rasu a makon da ya gabata, har yanzu ana alhinin rasuwarsa
- Ta wallafa bidiyo mai taba zuciya, tana cewa radadin mutuwar wadanda aka yi rayuwa da su baya taba gushewa daga zukata
- Mabiyan jarumar sun yi tsokaci kan bidiyon inda suka yi addu'o'i ga El-Muaz, suna rokon Allah ya karɓe shi cikin rahamarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Har yanzu, jarumar Kannywood Hadiza Gabon ta kasa mantawa da mawaki El-Muaz Birniwa wanda Allah ya yi wa rasuwa a makon jiya.
Legit Hausa ta ruwaito cewa El-Muaz ya yanke jiki ya fadi a wajen kwallon bikin mawaki Auta Waziri, kuma an sanar da rasuwar a asibiti.
Bidiyon Hadiza Gabon da marigayi El-Muaz
A cikin wani faifan bidiyo da jaruma Hadiza Gabon ta wallafa a shafinta na Instagram ta yi kalamai masu ratsa zuciya game da rasuwar El-Muaz.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadiza Gabon ta yi nuni da cewa mutane na zuwa suna tafiya, amma kuma radadin rashinsu ba zai taba gogewa daga zukata ba.
"Mutane na zuwa su tafi, ak an zo a daina tunawa da rayuwar baya, amma radadin rabuwar kan zauna a zuciya na har abada."
- A cewar Hadiza Gabon.
Wannan bidiyo da jarumar ta wallafa, ya ja hankalin mutane sosai, sama da mutane 15,000 suka nuna alamar soyayyarsu ga bidiyon.
Mutane sun yiwa marigayi El-Muaz addu'o'i
Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin maganganun da mutane suka yi a kan wannan bidiyo, wadanda mafi akasarinsu addu'o'i ne ga marigayi El-Muaz.
aliartwork:
"Allah ya jaddada rahama a gare shi."
badriyya_kalarawi:
"Allahu akhbar, El-Mu’az mutum ne mai kankan da kai, mai son wasa da dariya, mai faram faram da mutane. Allah ya sada shi da rahamarsa."
muffad_luxuries:
"Allah sarki. Wasu kuwa tuni sun manta da an yi wannan rashin, suna can suna sharholiya kamar ma babu abin da ya faru."
aishabashir8140:
"Wallahi na kasa manta rasuwar bawan Allah nan, na je ina ta ganin hirarrakin shi kamar yau aka yi su, amman wai baya duniyar ma baki daya. Allah ya ji kan mamatanmu."
Asiya Dambo:
"Allah ya sa ka dace amin, wannan dariya da kakeyi Allah yasa ka a Aljannah. Allah ya yi maka rahama. Amin ya rabbi."
ammah_83:
"Elmuaz kam mutumin ki ne. Allah ya gafarta masa ya sa ya huta, ya bamu guzurin iskosu na alheri."
Kalli bidiyon a kasa:
"Ba su mutunta El-Muaz ba" - Baba Shehu
A wani labarin, mun ruwaito cewa daraktan fina finan Hausa, Nasiru Ali Koki ya caccaki mawakan Kannywood da suka shirya casu bayan mutuwar El-Muaz Birniwa.
Nasiru wanda aka fi sani da Baba Shehu ya ce mawakan da suka shirya wannan casu sun nuna cewa ba su mutunta marigayi El-Muaz ba duk da gudunmawar da ya ba su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng