Mutuwar El Muaz Ta Bar baya da Kura: Sabuwar Matsala Ta Kunno kai a Kannywood
- Mutuwar mawaki El-Mu'az Birniwa ta tada kura, bayan mawakan Kannywood sun shirya casu kwanaki biyar kacal da rasuwar
- Darakta Nasiru Ali Koki ya nuna takaici kan mawakan da ba su mutunta marigayin ba, duk da gudunmawarsa a rayuwarsu
- Nasiru Koki ya ce El-Mu'az ya taimaka wa mawaka da yawa, amma da waɗanda suka ci moriyarsa ne aka shirya shagalin casun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Mutuwar fitaccen mawaki, El-Mu'az Birniwa ta bar baya da kura, inda mawakan Kannywood ke fuskantar matsala a halin yanzu.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa mawakan Kannywood sun shirya casu 'yan kwanaki kadan da rasuwar El-Mu'az Birniwa.
Wannan casu da suka shirya, ya jawo ce-ce-ku-ce mai zafi a masana'antar, musamman daga darakta Nasiru Ali Koki, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An caccaki mawaka kan shirya casu
Darakta Nasiru Ali Koki ya nuna takaicinsa kan yadda mawakan Kannywood din suka shafe idonsu da toka, suka shirya casu kwanaki biyar kacal da rasuwar Birniwa.
Daraktan ya ce akwai wadanda El-Muaz idan yana raye zai iya nuna su matsayin aminansa amma har da su ake tsalle ana dira a filin casun.
Legit Hausa ta tuntubi Nasiru Ali Koki, wanda ake kira da Baba Shehu domin samun karin haske game da maganar da ya yi da ta jawo ce-ce-ku-ce.
"Ba su mutunta El-Muaz ba" - Baba Shehu
Baba Shehu ya shaidawa wakilinmu cewa wasu abokan Kannywood abokan tsaro ne, ganin cewa basu damuwa da kai idan ka mutu.
A cewar Nasiru Ali Koki:
"Mu abin da muke gani shi ne, mutuwar ba ta taba su ba kuma bata dame su ba.
Ace mawaki dan uwansu, ya fadi ya rasu, a bikin mawaki dan uwansu, kuma su tafi su ci gaba da hidindimunsu, kamar ba su mutunta waka, mawaki da kuma dan uwansu ba.
"Ko ba komai, a matsayin El-Muaz na mawakin da ke nemowa mawaka kudi kuma yake mutunta waka, to ya kamata a sumunta shi."
"Akwai wadanda El-Muaz ya taimaka" - Nasiru
Baba Shehu ya ci gaba da cewa:
"Tun da casun nan kune kuka sanya ranar yinsa, kuna iya sanar da mutane cewa kun daga saboda mutuwar dan uwanku, wanda hakan ma zai iya jawo maku mutane.
"A cikin mutanen nan, kashi 9.9 sun mori El-Mu'az, kuma su ne suke tsalle suke dira a wajen casun. Akwai wanda ya ce Allah ya jikan El-Muaz Birniwa, a ci gaba da gashi.
"Na san mutanen da sun fi 20 wadanda idan El-Muaz ya daga waya ya ce gobe ku zo Kaduna ga harka ta samu, wallahi karfe 10 a Kaduna za ta yi masu."
An yi shagali a bikin Auta Waziri?
Shafukan sada zumunta sun cika da rade radin cewa an shirya shagali a bikin mawaki Auta Waziri duk da cewa El-Muaz ya rasu ne a wajen hidimar bikinsa.
Sai dai, Nasiru Ali Koki ya karyata wannan jita jita, yana mai cewa:
"Ina daya daga cikin wadanda suka shirya bikin Auta Waziri. Duk wanda ya ce maka an yi kida a bikinsa to bai yiwa Auta adalci ba.
"Walima kadai aka yi, kuma ita dama akwai ta a jadawalin bikin. Dama an shirya yin biki, kwallo, a nan ne El-Muaz ya r asu, za a yi kamu, washe gari 'cocktail'.
"Duk wadannan abubuwan bai yi ba. Auta walima ya yi, sannan kuma har aka yi aka gama ko kida ba ayi ba wallahi."
Allah ya yiwa El-Muaz rasuwa
Tun da fari, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar mawaki El-Muaz Birniwa a daren ranar Alhamis, 4 ga watan Disambar 2024 a jihar Kaduna.
An ce mawaki El-Muaz ya yanke jiki ya fadi a filin wasan kwallo lokacin da ake buga kwallon sada zumunci na bikin fitaccen mawaki Auta Waziri.
Asali: Legit.ng