Zargin Maɗigo: Ƴan Sanda Ɗauke da Makamai Sun Kama Fitacciyar Ƴar TikTok a Arewa

Zargin Maɗigo: Ƴan Sanda Ɗauke da Makamai Sun Kama Fitacciyar Ƴar TikTok a Arewa

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Momee Gombe ta yi karar Khadija Mai Bakin Kiss kan zargin bata mata suna da kazafin madigo
  • Momee Gombe ta jaddada cewa dole ta dauki mataki kan wannan kazafin saboda kare mutuncinta da na zuriyarta gaba daya
  • Bayan ta kwana a hannun 'yan sandan Kano, Khadija ta fito ta bayyana gaskiyar dalilin da ya sa ta yi wa jarumar kazafin neman mata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitacciyar jarumar Kannywood, Momee Gombe ta dauki mataki kan 'yar TikTok Khadija Mai Bakin Kiss game da bata mata suna da ta yi.

Khadija Mai Bakin Kiss ta zargi Momee Gombe da yin madigo da wata kanwarta Meema, har ta yi ikirarin cewa tana da bidiyon lalatar.

Momee Gombe ta yi magana yayin da 'yar TikTok ta zarge ta da madigo
Jami'an tsaro sun cafke 'yar TikTok da ta yiwa jaruma Momee Gombe kazafin madigo. Hoto: Momee Gombe, Mai Bakin Kiss
Asali: Facebook

A zantawarta da gidan rediyon Freedom Kano, jaruma Momee Gombe ta ce ta yi karar Khadija a ofishin 'yan sanda da ke Kano domin girman kazafin da aka yi mata.

Kara karanta wannan

Ana zargin fitacciyar jarumar Kannywood da neman mata? Ƴar TikTok ta ƙaryata kanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Momee Gombe ta sa an kama ƴar TikTok

Momee Gombe ta ce:

"Khadija ta fito ta yi magana a kan abin da ban sani ba. Ban san ta ba, ban taba mu'amala da ita ba. Sai na sa aka kama ta, na ce ta kawo bidiyo da muryar da ta ce tana da su."

Jarumar ta yi nuni da cewa, zargin da Khadija ta yi mata mai girman gaske ne, wanda idan ba ta dauki mataki ba zai iya bibiyarta har bayan ranta.

"Na sa aka kamata, amma ta zo tana ba ni hakuri, na ce mata ba maganar hakuri ba ce, saboda ina da 'yan uwa, iyaye, yayye, kuma ni mace ce, zan yi aure wata rana, zan haihu.
"Wannan abu na soshiyal midiya, zai iya daukar aru aru, wanda 'ya'yana za su iya gani. To shi ne na ce ta kawo hujjojin zargin da take yi."

- A cewar Momee Gombe.

Kara karanta wannan

Ya kamata ka sani: Manyan dalilai 4 da suka sa Rahama Sadau take shirya fina finai

"Na kwana a tsare" - Khadija 'yar TikTok

A nata bangaren, Khadija 'yar TikTok ta yi bayanin yadda ta kwana a hannun jami'an tsaro, inda a karshe ta yi belin kanta a kan N100,000.

Khadija ta ce:

"Ina wajejen titin gidan Zoo (Kano), sai wani mawaki ya kirani a kan zamu yi aikin kamfanin sola. Ina zuwa na zaro wayata iPhone, sai ga ma'aikata dauke da bindigu.
"Wallahi sai ga ma'aikata sun zagaye ni dauke da bindigu sun zagaye ni aka tafi tani. Sai da na kwana gari ya waye Momee ta zo, aka ce a kaimu kotu ko na ba ta hakuri."

Khadija ta ce gudun kada lamarin ya yi tsamari ya sa ta nemi ta bayar da hakurin inda ta dauki bidiyo ta yada a soshiyal midiya na neman gafarar Momee.

An wanke Momee Gombe daga zargi

Tun da fari, mun ruwaito cewa 'yar TikTok, Khadija Mai Bakin Kiss ta fito ta karyata kanta kan zargin da ta yiwa jaruma Momee Gombe na neman mata.

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu: APC ta fadi abin da zai faru da Atiku, Obi a zaben 2027

Khadija ta shaidawa duniya cewa ba ta da wani bidiyo ko sautin murya da zai zama hujja kan 'karyar' da ta yi wa Momee Gombe, tare da fadin dalilin yin kazafin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.