Ana Zargin Fitacciyar Jarumar Kannywood da Neman Mata? Ƴar TikTok Ta Ƙaryata Kanta

Ana Zargin Fitacciyar Jarumar Kannywood da Neman Mata? Ƴar TikTok Ta Ƙaryata Kanta

  • 'Yar TikTok, Khadija mai bakin 'kiss' ta fito ta karyata wani ikirari da ta yi na cewa tana da bidiyon Momee Gombe tana madigo
  • A 'yan kwanakin nan, soshiyal midiya ta dauki zafi tun bayan da aka fara yada zargin cewa jarumar Kannywood tana neman mata
  • A wani sabon bidiyo da aka fitar, an ga Khadija tana ba Momee Gombe hakuri, yayin da take wanke ta daga wannan babban zargi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - An shiga rudani a masana'antar Kannywood yayin da aka zargi fitacciyar jaruma, Momee Gombe da neman 'yar uwatarta mace.

Wannan zargi ya jawo ce-ce-ku-ce mai zafi daga 'yan masana'antar, har dai Allah ya sa gaskiya ta fito daga bakin Khadija mai bakin 'kiss.'

Khadija mai bakin kiss ta yi magana kan zargin madigo da ake yiwa Momee Gombe
Khadija mai bakin kiss ta wanke Momee Gombe daga zargin madigo. Hoto: momee_gombe
Asali: Instagram

A wani faifan bidiyo da mai ba da umarni a Kannywood, Sheikh Isah Alolo ya wallafa a shafinsa na Instagram, an ga Khadija ta na fadin gaskiyar abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu: APC ta fadi abin da zai faru da Atiku, Obi a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene ya jawo ake zargin Momee Gombe?

A wani bincike da Legit Hausa ta yi, ta gano cewa 'yar TikTok, Khadija mai bakin kiss ce ta fara fitar da wani bidiyo, inda take zargin Momee Gombe da neman mata.

A cikin bidiyon da ya karade shafin TikTok, an ga Khadija tana cewa tana da bidiyon da ya nuna jarumar tana neman 'yar uwarta mace, amma sai an biya ta kudi kafin ta tura.

Wannan ya jawo martani daga 'yan TikTok, musamman Hassan Make-Up wanda ya fara fitowa ya karyata Khadija akan wannan ikirari da ta yi.

Khadija ta wanke Momee Gombe daga zargi

To sai dai 'yan kwanaki bayan bullar bidiyon Khadija, sai kuma aka sake ganin 'yar TikTok din ta fito ta karyata wancan ikirari da ta yi, tare da wanke jaruma Momee Gombe.

A cikin sabon bidiyon, Khadija mai bakin kiss ta shaidawa duniya ba ta da wani bidiyo na zargin da ake yiwa Momee, kuma ta yi maganar ne don neman mabiya a shafinta.

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

Khadija wadda aka nunata a cikin wani falo tare da Momee Gombe, ta nemi afuwar jarumar tare da cewa:

"Don Allah Momee ki yi hakuri, tuba nake yi masoyiya. Ban taba saninkina da kirki ba sai yau da kika ce kin yafe mani, babu komai."

A gefe daya kuma, an ga Momee Gombe a zaune, inda ta ce "ba komai" bayan Khadija ta nemi gafararta.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin jaruma Momee Gombe kan wannan lamari ya ci tura, yayin da wayarta ba ta shiga, kuma ba ta dawo da amsar sakon WhatsApp ba.

Kalli bidiyon a kasa:

"Gwanja abokin sana'ata ne' - Momee Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Momee Gombe ta warware rudanin da aka samu biyo bayan wasu zafafan hotuna da ta dauka tare da mawaki Ado Gwanja.

Jarumar Kannywood wadda ta fi fitowa a bidiyon wakoki ta ce ko kadan babu alakar soyayya tsakaninta da Ado Gwanja, shi din abokin sana'arta ne kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.