Bidiyo: Ana Jimamin Mutuwar El Muaz, Mawaki Adam A Zango Ya Hada Gagarumin Casu
- Fitaccen mawakin Hausa, Adam A Zango ya nishadantar da daruruwan masoyansa a wani babban taron casu da ya shirya
- A wajen taron casun, an ga su G-Fresh Al'Ameen da wasu mawakan yayin da Adamu Zango ke rera fitattun wakokin da ya yi
- Ma'abota shafukan sada zumunta, musamman masu bibiyar mawaki Zango sun yi tsokaci kan bidiyon casun da ya wallafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fitaccen mawaki kuma jarumin Kannywood, Adam A. Zango ya gabatar da wani babban casu ga masoyansa bayan dogon lokaci yana hutu.
Wannan baban casu da Adam A Zango ya shirya tare da wasu mawaka kamar G-Fresh Al'Amin na zuwa ne kwanaki da rasuwar mawaki El-Muaz Birniwa.
Adam A Zango ya wallafa wasu fafayan bidiyo hudu a shafinsa na Instagram inda aka ganshi yana nishadantar da daruruwan mahalarta taron da wakokinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adam A Zango ya shirya babban casu
Mawaki Adamu Zango wanda dan asalin jihar Kaduna ne ya dade yana sharafi a fagen wakokin soyayya kafin daga bisani ya koma harkar fim gadan gadan.
A faifan bidiyo na farko, Adam A Zango ya rera daya daga cikin fitattun wakokinsa mai taken 'Gumbar Dutse' wadda aka ce habaici ce ga masu adawa da sharafinsa.
'Ai rawa da tsari' ita ce waka ta biyu da Adam A Zango ya rera a wajen casun, an ga mawaki G Fresh Al'Amin a cikin bidiyon yana taya Zango rera wakar.
Mutane sun yi tsokaci kan casun Adam Zango
Haka zalika, an ga G-Fresh a bidiyo na uku da Zango ya wallafa, amma ba a ganshi a na hudu ba, wanda ya sa mutane tambayar abin da ya kai G-Fresh taron.
Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin mutane kan wannan casu da Adam A Zango ya shiya.
abubakar_sadiq6078:
"Allah ya sa mu cika da imani. Wato babu wani abin da za a fasa idan ba ka da rai."
waleed_alanso"
"Wai shi G-fresh menene shi a wajen taron, ko dakko sa aka yi a biyasa?"
__al_huzaifii_:
"Yariman wannan lokaci."
bachob40_227:
Idan an girma dai a san an girma, a kasar Hausa muke ba kasar turawa ba."
ahmad_textile_ngr_ltd:
"Muna godiya Zango, Allah ya huce gajiya."
Za a haska fim din Hausa a Saudiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa masana'antar Kanywood ta sake samun karbuwa a duniya yayin da aka shirya haska fim din Hausa a kasar Saudiya.
Za a haska fim din mai suna 'Mamah' wanda Rahama Sadau da Abdul Amart (Mai Kwashewa) suka shirya a wajen bikin baje kolin fina finai da ke birnin Jedda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng