Yan Sanda Sun Wanke Jarumar Fina Finai daga Zargin Satar Zinari, an Gano Dalili

Yan Sanda Sun Wanke Jarumar Fina Finai daga Zargin Satar Zinari, an Gano Dalili

  • Rundunar yan sanda a Lagos ta magantu kan zargin satar zinari da ake yi wa fitaccen jarumar fina-finai a jihar
  • An zargi Lizzy Anjorin-Lawal da satar zinari da damfara a kasuwar Oba Akintoye da ke jihar Lagos bisa kuskure
  • Kakakin rundunar yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa babu zargin satar da ake yi wa Anjorin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Rundunar yan sanda a jihar Lagos ta wanke jarumar fina-finai kan zargin sata da kuma damfara a kasuwa.

Rundunar ta ce babu hujjoji kan zargin Lizzy Anjorin-Lawal da satar zinari a kasuwar Oba Akintoye a Lagos.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

Yan sanda sun wanke jarumar fina-finai a Najeriya
Rundunar yan sanda ta wanke jarumar fina-finai, Lizzy Anjorin kan zargin sata. Hoto @lizzyanjorin_original.
Asali: Instagram

Yan sanda sun magantu kan zargin jarumar fim

Kakakin rundunar yan sanda a Lagos, Benjamin Hundeyin shi ya tabbatarwa wakilin Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hundeyin ya ce faifan bidiyo da ake yada Anjorin da zargin sata ba gaskiya ba ne kwata-kwata.

Ya ce sun tabbatar da kammala bincike kan lamarin, kuma sun wanke jarumar kan zargin da ake yi mata.

'Babu gaskiya a zargin Anjorin' - Yan sanda

"Babu wani zargi kan Anjorin game da satar zinari, mai kayan ne ya ba da lambobin asusun banki ba daidai ba."
"Bincike ya tabbatar da cewa Anjorin ta tura kudi zuwa asusun bankin wanda aka ba ta ba daidai ba."
"Bayan an gano an yi kuskuren zargin Anjorin, ta yi korafi inda aka cafke wanda ake zargin da kuma kai shi kotu, daga bisani ta janye karar a radin kanta."

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyya: An bayyana lokacin da Damagum zai sauka daga shugaban PDP

- Benjamin Hundeyin

Jarumar fim, Nwachikwu ta fadi karfin sha'awarta

Kun ji cewa cikin karfin gwiwa, jarumar fina-finan Nollywood, Esther Nwachukwu ta bayyana wasu bayanai masu rikitarwa game da rayuwarta.

A wata zantawa da aka yi da tauraruwar fina-finan a shirin 'Honest Bunch', jarumar ta bayyana irin karfin sha'awa da take da shi a rayuwa.

Ta kuma ba da taƙaitaccen bayani game da garuruwa da ƙasashen da ta je ta yi lalata da mazajen da suka kai kimanin 3000 a cikin shekaru 30.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.