Jarumin Kannywood, Adam Zango Ya Samu Babban Mukami, Ali Nuhu Ya Fito Ya Yi Magana
- Shahararren jarumi kuma mawaki a masana'antar Kannywood, Adam A Zango ya zama babban darakta na gidan talabijin Qausain
- A cikin wata sanarwa da shugaban rukunin kamfanonin Qausain, Nasir Idris, ya fitar, an ce nadin Zango zai fara aiki ne a nan take
- Hakazalika, rukunin kamfanonin Qausain ya nada Isa Pantami a matsayin darakta mai zaman kansa domin ba da shawarwari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Rukunin kamfanonin Qausain, ya nada fitaccen jarumin nan kuma mawakin Kannywood, Adam A. Zango a matsayin babban darakta a gidan talabijin din Qausain.
An bayyana wannan nadin a cikin wata sanarwa da shugaban rukunin kamfanonin Qausain, Alhaji Nasir Idris, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Adam A Zango ya zama darakta janar
A cewar sanarwar, an amince da nadin ne yayin wani taron kwamitin gudanarwar rukunin kamfanonin a ranar Juma'ar da ta gabata, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Nasir Idris ya ce nadin mukamin da aka yi wa Adam A Zango zai fara aiki nan take domin ba jarumin damar fara jan ragamar gidan talabijin din na Qausain.
A yayin da ake fatan jarumin zai yi amfani da kwarewarsa wajen kawo shirye shiryen da za su karbu a wajen al'umma.
Baya ga haka, sanarwar ta ce an nada Adam A. Zango ne saboda irin hazakarsa.
Pantami ya samu mukami a Qausain
Hakazalika, sanarwar ta ce an nada tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Pantami a matsayin darakta mai zaman kansa.
"A matsayinsa na darakta mai zaman kansa, Pantami zai rika ba da shawarwari da kuma kalubalantar hukunce-hukuncen hukumar gudanarwar a kokarin inganta ayyukanta.
"An tsara matsayin Farfesa Isa Pantami ne domin tabbatar da cewa dukkanin matakan da hukumar gudanarwar ta dauka ba su ci karo da ra'ayin wani na kashin kai ba."
- A cewar sanarwar.
Ali Nuhu ya taya Adam Zango murna
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram, shugaban hukumar fina finan Najeriya, Ali Nuhu ya taya Adam A Zango murnar wannan mukami da ya samu.
"Ina tayaka murna Baba @adam_a_zango, Allah ya rika maka."
- A cewar Ali Nuhu.
Qausain: An karrama Farfesa Pantami
A wani labarin, mun ruwaito cewa Farfesa Isa Ali Pantami wanda tsohon minista a Najeriya ne ya samu lambar yabo daga gidan talabijin na Qausain.
Hukumar gidan talabijin bisa jagorancin shigabanta, Mallam Nasir Albanin Agege ne ta ba shi wannan lambar yabo na gwanintar aiki a birnin Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng