Masana'antar Fina Finai Ta Sake Shiga Jimami Bayan Rasuwar Fitaccen Jaruminta
- Yayin da ake ci gaba da rasa fitattun jaruman fina-finai, a yau Juma'a an sake sanar da mutuwar wani jarumin a Legas
- Fitaccen jarumin fina-finan Yarbawa, Ganiyu Oyeyemi wanda aka fi sani da Ogunjimi ya riga mu gidan gaskiya a yau
- Jarumin fina-finai, Kunle Afod shi ya tabbatar da mutuwar fitaccen jarumin a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu a shafin Instagram
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Masana'antar shirya fina-finan Nollywood ta sake shiga jimami bayan mutuwar fitaccen jaruminta.
An wayi garin yau Juma'a 26 ga watan Afrilu da mutuwar shahararren jarumin fina-finai, Ganiyu Oyeyemi.
Yaushe jarumin fina-finan ya rasu?
Marigayin wanda aka fi sani da Ogunjimi ya rasu ne a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu bayan fama da jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumin Nollywood, Kunle Afod shi ya tabbatar da rasuwar marigayin a shafinsa a Instagram a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu.
Afod ya ce tabbas masana'antar shirya fina-finan ta tafka babban rashin fitacce kuma jajaritacce.
"Mun yi iya bakin kokarinmu amma Ubangiji ya fi mu sonka, muna maka fatan samun rahama Baba Ogunjimi."
- Kunle Afod
Shura da fitaccen jarumin fina-finan ya yi
Marigayin ya yi kaurin suna a fina-finan jarumta a bangaren yaren Yarbanci inda da ya fito a manyan fina-finai.
Har ila yau, jarumin kafin rasuwarsa yana yawan fitowa a fina-finan tsafi da kuma maita.
Mace-macen taurarin fina-finai a Najeriya
Wannan na zuwa ne yayin da masana'antar shirya fina-finai ke cikin jimamin rashe-rashen da ta yi a cikin kwanaki.
Masana'antar ta tafka manyan rashe-rashe na jarumanta da dama tun farkon wannan shekara da muka ciki.
Tsohon sanata ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, kun ji cewa tsohon sanata a Najeriya, Ayogu Eze ya riga mu gidan gaskiya a birnin Tarayya Abuja.
Marigayin wanda ya wakilci mazabar Enugu ta Arewa daga shekarar 2007 zuwa 2015 ya rasu ne a jiya Alhamis 25 ga watan Afrilu.
Sanatan ya ba da gudunmawa sosai a Majalisar Dattawa inda ya kasance daya daga cikin mambobin kwamitin gyara kundin tsarin mulki.
Asali: Legit.ng