Ku Shakata a Karshen Mako da Shiri Mai Dogon Zango ‘Buri’ a Tashar Africa Magic Hausa

Ku Shakata a Karshen Mako da Shiri Mai Dogon Zango ‘Buri’ a Tashar Africa Magic Hausa

Tashin hankali ya samu attajirin dan kasuwa, Abu Mansur, a lokacin da ya farfaɗo daga rashin lafiya tare da mance rayuwarsa baya.

Tashar Africa Magic Hausa ta yi alkawarin debe muku kewa da kayataccen shiri mai dogon zango, Buri a kowanne karshen mako.

Shirin Buri yana dauke da fitattun jarumai irinsu Tahir Fagge, Zainab Barka, Kamilu Ibrahim da dai sauransu.

Shirin Buri mai dogon zango
Yadda za a haska shirin Buri a Africa Magic Hausa
Asali: Original

Wadannan jarumai ne suka hadu a shirin da ke nuna faftukar rayuwar Abu Mansur a tsakiyar cin amanar da aka masa a rayuwa.

A cikin shirin, ya kasance cikin dinuwar cutar mantau da ke bibiyarsa, wacce ya da damu matuka da samun waraka.

Sabon yanayin da ya shiga ya jefa shi cikin fargaba. A wannan hali na tsaka mai wuya, sai aka samu dangi da ke shirin tabbatar da ganin bayansa tare da wawure dukiyarsa.

Wannan yasa Abu Mansur barin gidansa tare da buya har zuwa lokacin da zai sake shirin ci gaba da rayuwa kamar yadda ya saba.

Duk da haka, Abu Mansur na bukatar yin faftukar neman makusanta masu amana da za su taimakawa halin da yake ciki.

Amma duk sadda magana ta fara nisa tsakaninsa da duk wanda ya gamu dashi, rashin yarda ke kara habaka. Ta yaya zai fice daga wannan kitimurmur?

Za ku iya sanin yadda ta kaya a tsakanin ranakun Alhamis zuwa Lahadi da misalin karfe 7:30 na dare a Africa Magic Hausa (DStv ch 154 da GOtv ch 4).

Don kallon shirye-shiryen baya daga shirin na Buri, ku kasance da tare da tashar a DStv da GOtv. Za ku iya sauke manhajar MyDStv ko MyGOtv ko kuma ku latsa *288# a wayoyinku don shiga tsarin.

Baya ga shirin Buri, masu kallo na sha'awar kallon fina-finai irinsu Al'ada, Aminullah, Arewa Game Show da sauran shirye-shirye masu kayatarwa a tashar Africa Magic Hausa ta kafar GOtv.

{TALLA}

Asali: Legit.ng

Online view pixel