Alƙalin Kotun Musulunci ya ɗage shari'ar jaruma Hadiza Gabon saboda matarsa bata da lafiya
- Alkalin Kotun Shari'ar Musulunci da ke Magajin Gari Kaduna ya ɗage zaman shari'ar Hadiza Gabon saboda matsalar rashin lafiya
- Alkalin ya nemi uzurin cewa ya samu labarin an garzaya a matarsa Asibiti a Zariya, don haka ba zai iya maida hankali kan ƙarar ba
- Wani ma'aikaci ya maka Gabon a gaban Kotun ne bisa zargin ta ƙi cika masa alkawarin da ta ɗauka na aure
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Alƙalin Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna, Khadi Rilwanu Kyaudai, ya ɗage cigaba da zaman shari'ar fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon.
An ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 1 ga watan Agusta, 2022, biyo bayan rashin lafiyar da matar Alƙalin ke fama da ita, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Wani ma'aikaci mai suna Musa, ya gurfanar da jarumar a gaban Kotu kan zargin ta ƙi cika masa alƙawarin da ta masa na aure bayan ya kashe mata kuɗi N396,000.
'A haife shi a 1958, ya fara makaranta 1959?' Sabbin matsaloli da suka taso kan takardun sabon shugaban Alkalai
Sai dai Hadiza Gabon ta musanta ƙulla kowace irin alaƙa da mutumin a zaman Kotu na ƙarshe ranar 14 ga watan Yuni, 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa dukkan ɓangarorin biyu sun halarci Kotun yau Talata, lokacin da Alƙali ya sanar da cewa yanzu ya samu labarin an kwantar da ɗaya daga cikin matansa a Asibitin Zariya.
Bisa haka Alƙalin ya bayyana cewa ba zai iya cigaba da sauraron ƙarar ba saboda zuciyarsa na can kan halin da matarsa ke ciki.
Ya ce:
"Ku yi hakuri da ni saboda ba zan iya sauraron ƙarar nan ba a yau. Yanzun na samu labarin ɗaya daga cikin matana bata da lafiya, ina buƙatar gaggauta zuwa gida."
Ya bangarorin suka ɗauki matsalar?
Da yake jawabi jim kaɗan bayan haka, Lauyan wanda ke ƙara, Murtala, ya ce an ɗage zaman saboda halin da matar alƙali take ciki.
Lauyan ya ce:
"An kira Alkali daga Zariya cewa matarsa na Asibiti kuma wajibi ne mu masa uzuri, ya faɗa mana idan muka matsa a cigaba da zaman ba zai iya maida hankali ba. Ya ɗage zama zuwa 1 ga watan Agusta."
A ɗaya ɓangaren kuma lauyan Jaruma Hadiza Gabon, Barista Mubarak Sani Jibril, yace tawagarsa ta amince da ɗage zaman, ya kuma roki Allah ya ba matar Alƙali lafiya.
A wani labarin kuma Jerin sunayen Jaruman Kannywood uku da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023
Wasu daga cikin Jaruman Kannywood da tauraruwarsu ke haskawa sun bayyana tsayawa takarar siyasa a zaɓen 2023.
Mun tattaro muku waɗan nan jaruman da suka nuna sha'awar ba da gudummuwarsu a ɓangaren shugabancin al'umma a Najeriya.
Asali: Legit.ng