A karon farko, Jaruma Hadiza Gabon tayi martani ga masu cewa tana kyautar Riya
- Daga cikin jaruman Kannywwood masu matukar taimako akwai Hadiza Aliyu gabon, wacce ta yi fice wurin taimakon marayu da masu karamin karfi
- Sai dai jarumar na shan caccaka inda suke cewa riya take yi ko kuma su ce babu lada sadaka da kudin karuwanci duk da basu da shaida kwakwara
- A wannan karon, Gabon ta wallafa bidiyon da ke magana kan munafukai masu irin wannan halin inda ta yi shuguben cewa, "Ana magana fa"
Sanannen abu ne cewa jaruma Hadiza Gabon tana daya daga cikin jarumai a masana'antar Kannywood masu matukar taimakawa bayin Allah dake cikin damuwa.
Cikin irin taimakon da Hadiza Gabon tayi da yafi daukar hankali shine na wani dattijo mai suna Abba Babuga wanda ruwa ya cinye gidansa, yana zaune a ciki bashi da inda zashi kuma bashi da kudin ginawa. Hadiza Gabon din ce ta dauka nauyin gina masa gidan.
Har ila yau, akwai wani dattijo da aka taba yada bidiyonsa yana bayyana soyayyarsa ga jarumar wanda maimakon ta fusata, sai ta fahimci yana bukatar taimako, hakan yasa ta aika masa da N200,000 kyauta tare da bayyana masa cewa shi ai uba yake gareta amma idan auren ya taso za ta aika masa da gayyata, lamarin da yayi matukar birge masoyanta.
Baya ga nan, akwai lokacin da jarumar ta gina masallaci katafare a wata anguwa. Hakan ya janyo mata addu'o'i masu yawa daga jama'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba a nan jarumar ta tsaya ba, ta kan bi makarantu da gidajen marayu tana kai tallafin na tufafi da sauran kayan bukata duk a karkashin gidauniyarta mai suna Hadiza Gabon Foundation.
Duk da wadannan taimakon da jarumar ke yi, bai hana ta shan zagi ba daga wasu ma'abota kafafen sada zumunta inda suke cewa sadaka da kudin karuwanci babu lada ko kuma su ce riya ce da sauran maganganu marasa dadi da jarumar ke shanyewa.
A karo na farko, jarumar ta tanka wa masu irin wannan maganganu inda ta wallafa wani bidiyon Sheikh Kabiru Gombe wanda yake bayani kan munafukan da kan yi ta maganganu idan mutum ya yi aikin alkhairi su ce riya ce ko kuma idan mutum ya bada kadan su ce ya yi kadan babu lada, alhalin ko sisi basu bada ba.
Ga dai abinda malamin ke cewa:
Bayan Hadiza ta wallafa wannan bidiyon, a kasa ta kara da cewa:
"Ana magana da ku, kuna ina?" Ta hada da alamar dariya.
"Yauwa, kafin ku dame ni a sashin tsokaci da emoji, ku saurari maganar tukunnna. Kada ku cika min sashin tsokaci da alamun wuta ko zuciya."
Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah
A wani labari na daban, a daren ranar Asabar ne wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da aka fara gininsa tun daga tushe har aka kammala shi.
Bawan Allan ya wallafa, "Alhamdulillah, wannan ne masallacin da jaruma Hadiza Gabon ta ginawa bayin Allah domin yin sallah fisabilillah.
"Ginin ya kammala kuma muna mata addu'ar Allah ta'ala yasa mata a mizaninta, ya kuma saka mata da alkhairi, ya ji kan mahaifinta Malam Aliyu Diya."
Asali: Legit.ng