Ku daina haihuwar yara birjik idan kun san ba za ku iya kula da su ba – Nafisa Abdullahi
- Jaruma Nafisa Abdullahi ta nuna bacin ranta yadda wasu iyaye ke zubar da kananan yara a titi da sunan tura su almajiranci
- Yar wasar ta shawarci iyaye da su daina haihuwar 'ya'ya da yawa idan sun san basu da halin kula da su
- Nafisa ta kuma bayyana cewa sai Allah ya sakawa wadannan yara domin babu amfanin ci gaba da sako su ba tare da tanadi ba
Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta yi jan hankali ga mutanen da ke haihuwar yara da yaw aba tare da basu kulawar da ta dace ba.
Nafisa ta bukace su da su guji aikata hakan a cikin wata wallafa da ta yi a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu.
Har wayau, jarumar ta bayyana cewa Allah zai tuhumi mutanen da suke haihuwar yara ba tare da sauke nauyin da ya dora musu ba.
Ta rubuta a shafin nata:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ku daina haihuwar yaran da kuka san ba ku da halin kula da su."
"Kun ga dukkan mutanen da ke haifar 'ya'yan da ba su ji ba ba su gani ba, domin kawai su aika da su almajiranci, sannan su ci gaba da haifar karin 'ya'ya, Allah sai ya saka wa yaran nan!!!"
Ta nuna bacin ranta matuka kan yadda wasu iyaye ke tura 'ya'yansu masu shekara biyu zuwa uku almajirci.
Ta kara da cewa:
“Me yaro dan shekara 2/3 yake yiwa almajiranci? Kamar menene dalilin?”
Jama'a sun yi martani kan batun
@danbatta_auwal ya yi martani:
"Tarbiya da kuma Kula da Yara na wuyan iyaye lallai Yana da matuqar muhimmanci muhankalta"
@DogoHusaini ya ce:
"Gaskine nima banga wani soyayya ko jiƙai ba a cikin hakan,musamman a yanzu da rayuwa ke cike da haɗurra.
"Ko Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ƴaƴanku abin kiwone a gareku kuma za a tambayeku a kan kiwon nasu."
@BbkShettima ya ce:
"Kin fadi abun a yadda yake. Gaskiya iyayen yaranan basu kyauta ba."
Gaskiyar abun da ya raba aurena da Fati Mohd – Sani Musa Mai Iska
A wani labarin, tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa kuma miji ga tsohuwar jaruma, Fati Muhammad, Sani Musa Mai Iska ya magantu a kan abun da ya kawo rabuwar aurensu a shekarun baya.
Mai Iska ya tuno yadda aurensu ta kasance da Fati wacce suka lula suka bar kasar zuwa Ingila yan watanni bayan bikin nasu sakamakon samun damar shiga wani shiri na wayar da kai kan Kanjamau da ita jarumar ta yi.
Jarumin ya ce bayan sun je kasar Ingila sun kammala shirin, sai suka dawo gida Najeriya amma sai shi ya sake komawa kasar saboda wani dalili nasa na gashin kansa. Ana haka sai ya ga cewa zai fi samun nutsuwa idan matarsa na kusa da shi don haka ya nemi Fati ta dawo kasar ita ma.
Asali: Legit.ng