Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

  • Babbar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Maryam Booth ta bayyana cewa mutane na yawan tambayarta yaushe za ta yi aure da me yasa ta rame
  • Maryam ta ce aure nufi ne na Ubangiji kuma sai lokacin da ya tsarawa mutum ya kai kafin ya yi shi
  • Jarumar ta kuma ce dalilin ramar da tayi baya rasa nasaba da jinya, damuwa da rashin mahaifiyarta da ta yi

Shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Adamu wacce aka fi sani da Maryam Booth ta magantu a kan wasu tambayoyi biyu da mutane ke yawan yi mata wanda a cewarta ta gaji da amsa su.

A wata hira da aka yi da ita a shirin BBC Hausa mai suna ‘Daga bakin mai ita’ jarumar ta ce mutane na yawan yi mata tambayar yaushe za ta yi aure ko kuma menene yasa ta rame.

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame
Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Amsoshin da nake bayarwa a duk lokacin da aka yi mun tambayoyin

Da aka tambaye ta kan amsar da take bayarwa a duk lokacin da aka yi mata su, sai jarumar ta ce:

“Tambayar farko yaushe za ki yi aure? Shi aure nufi ne na Ubangiji, kuma duk yadda ka kai ga shirin aure idan Allah bai yi lokacin nan ba toh babu yadda za kayi. Sannan kuma yadda mutum bai san ranar haihuwarsa ba kuma bai san ranar mutuwarsa ba, hakazalika mutum babu wanda ya isa ya ce ga ranar aurenka.
“Koda yau ka zo ka sa lokaci ka ce rana ita yau zan daura aure idan Allah bai yi ba, toh babu abun da zai kawo shi. Na san mutane za su ce ai kaima baka yi niya ba, haka ne komai niya ce ko bah aka ba? Amma kuma koma menene idan Allah bai yi ba fa? Wani za ka ga bai da babban buri a rayuwarsa illa ya yi auren kuma idan Allah ya yi ba lokacinka bane babu yadda za a yi ka yi auren.

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

“Sannan zancen me yasa na rame. Idan ka duba ramar da na yi na gabannin wani dan lokaci ne, sannan duk wanda ya sanni ya san alakata da mahaifiyata kuma ya san zamantakewarmu. Rashin lafiyarta, jinyarta da damuwa, da kuma rasata da nayi dole na rame amma Alhamdulillah ba wai hakan ya hana ni tawakkali ba. Na yi tawakkali.”

Ana yawan yi mun gori da na ki yin aure amma na san Allah bai manta da ni ba - Fati Slow

A wani labari makamancin wannan, fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Slow Motion ta bayyana cewa mutane na yawan yi mata gori kan rashin yin aure.

A wata hira da sashin Hausa na BBC ta yi da ita a shirin 'Daga bakin mai ita', Fati ta ce aure lokaci ne kuma ta san Allah bai manta da ita ba.

Kara karanta wannan

Wata mata a Nasarawa: Dalilin da yasa na amince 'dan da na haifa ya dirka min ciki

Tsohuwar jarumar fim din ta ce aure nufi ne na Ubangiji don haka idan ya nufa za ta yi toh babu makawa za ta yi shi, sannan cewa idan Allah bai tsara zata yi aure ba a rayuwarta toh babu wanda ya isa ya daura mata shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng