Ana yawan yi mun gori da na ki yin aure amma na san Allah bai manta da ni ba - Fati Slow
- Tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Fati Slow Motion ta bayyana cewa jama'a na yawan yi mata tambaya da gori kan cewa ta ki yin aure
- Fati ta ce aure lokaci ne kuma ta san Allah bai manta da ita ba
- Ta kuma ce idan Allah ya nufa za ta yi aure kafin ta amsa kiransa toh za ta yi, amma idan bai shirya aure a rayuwarta ba babu wanda ya isa ya daura mata shi
Fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Slow Motion ta bayyana cewa mutane na yawan yi mata gori kan rashin yin aure.
A wata hira da sashin Hausa na BBC ta yi da ita a shirin 'Daga bakin mai ita', Fati ta ce aure lokaci ne kuma ta san Allah bai manta da ita ba.
Tsohuwar jarumar fim din ta ce aure nufi ne na Ubangiji don haka idan ya nufa za ta yi toh babu makawa za ta yi shi, sannan cewa idan Allah bai tsara zata yi aure ba a rayuwarta toh babu wanda ya isa ya daura mata shi.
Da BBC ta tambaye ta game da tambayar da ta gaji da amsawa, sai Fati Slow ta ce:
“Tambayar da na gaji da amsawa da kuma ake yawan yi mun gori da ita itace yaushe za ki yi aure?, kin ki yin aure. Ni kuma na dauka kamar da mutuwa da aure kamar duk lokaci ne.
"Na san cewar Allah bai manta da ni ba, koma menene na san Allah bai manta da ni ba. Idan Allah ya yi zan yi aure kafin in mutu zan yi, idan Allah ya yi ba zan yi aure ba zan koma ga rabbi-ssamawati ban yi aure ba toh wallahi babu wanda ya isa ya daura mun aure. Alkawari ne na Ubangiji sai lokacin da ya cika shi."
Da aka tambaye ta game da amsar da take bayarwa idan aka yi mata tambayar, jarumar ta ce:
“Dama amsa ce kwaya biyu. Ka san ranar da za ka mutu? Idan kace mun baka san ranar da za ka mutu ba, toh shikenan magana ya kare."
Naziru sarkin waka ya cire mun kebura 99 a jikina – Fati Slow
A gefe guda, Fati ta magantu a kan yadda aka kai karshen takkadama da ya faru a masana'antar ta shirya fina-finan Hausa kwanakin baya a hirarta da BBC Hausa.
Jarumar ta bayyana cewa masana'antar fim ta yi masu uwa ta yi masu uba shiyasa ta fito ta yi magana tun farko.
Fati ta bayyana cewa komai ya zo karshe ne bayan Naziru sarkin waka ya tsamo ta daga yanayi na kebura (talauci) da take ciki domin a cewarta, sai da ya cire mata kebura 99 daga jikinta.
Asali: Legit.ng