Jarumar Kannywood Ladin Cima: Ban taba samun sama da N5k a harkar fim nan take ba

Jarumar Kannywood Ladin Cima: Ban taba samun sama da N5k a harkar fim nan take ba

  • Jarumar Kannywood, Ladin Cima Haruna, ta magantu kan yadda ta tsinci kanta a masana'antar shirya fina-finai
  • Ladin Cima ta ce ta fara fim bayan rasuwar mijinta a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon
  • Sai dai kuma jarumar ta ce duk da dadewar da ta yi a wannan harka, ba a taba bata kudi sama da N5,000 ba idan ta fito a fim

Shahararriyar jarumar Kannywood wacce ke fitowa a matsayin Uwa da Kaka, Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya ta bayyana wasu abubuwa game da kanta tun daga lokacin da ta fara harkar fim.

Ladin Cima ta ce ta fara harkar fim ne bayan rasuwar mijinta a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon. A cewarta tana da shekaru 18 a zamanin.

Kara karanta wannan

Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

A hira da tayi da sashin Hausa na BBC, jarumar ta ce ta fara dirama ne tun suna zuwa Kaduna domin a lokacin babu yan fim a Kano, inda ta ce ba a biyansu ko sisi a lokacin illa kawai suna aikin ne saboda sha’awarsu ga aikin.

Jarumar Kannywood Ladin Cima: Ban taba samun sama da N5k a harkar fim nan take ba
Ladin Cima ta ce bata taba samun sama da N5k a harkar fim nan take ba Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sai dai kuma, ta ce tsawon lokacin da ta dauka tana fim, ba ta yi fim din da za a dauko N20,000 ko N30,000 ko N50,000 a bata ba inda ta ce ana biyanta daga N2,000 zuwa N5,000 idan ta yi fim.

Ga yadda hirarta da BBC ta kaya:

"Harkar fim da na fara bayan mutuwar mijina ce, a lokacin saboda ina gidan miji talbijin fara ce ba mai kala ba,toh kawai wasu abubuwa da nake gani a talbijin sai yake bani sha’awa. Bayan mijina ya mutu kawai sai na fada harkar dirama.

Kara karanta wannan

Ni nan na bata N40k a fim din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cima

“A lokacin da na fara fim, Kaduna ake zuwa babu yan fim a Kano sai a Kaduna, toh za mu je ranar Juma’a sai mu dawo ranar Lahadi. Kuma ba kudi ake biyanmu ba, abinci ma ranar da muka je ake bamu, daga shi mu za mu je mu siya abincinmu mu ci amma Allah Allah muke yi Juma’a ta zo mu tafi Kaduna."

Game da fim din da ta fara fitowa, Cima ta ce:

“Akwai wani fim shine fim dina na farko Shehu Goma.”
“A lokacin kin san idan kana son abu, ka kan nemi wadanda suke yin abun, toh ta haka ne na shiga fim din. Akwai wata kawata Cima don da ita take zuwa a matar mallam Bappa, ta dalilinta ne sai na shiga wannan dirama. Lokacin za a yi fim din Shehu Goma su zasu tafi Nijar mu kuma sai muka yi a nan Kano."

Game da kalubalen da ta taba fuskanta a harkar fim, Ladi ta ce:

Kara karanta wannan

'Yar Bokon gaske: Yadda matashiya ta kame kanta, ta kammala digiri da CGPA 7.0

"Alhamdulillahi tun daga lokacin da na fara wannan harka daga NTA Kaduna zuwa NTA Kano kawo yanzu a Kannywood ban taba haduwa da matsala ba sai a bana wannan shekarar. Na gamu da matsala wacce ni kadai ce na san ta amma daga baya duk na gayawa al'umma saboda sai da na nemi taimako. Allah ya taimaka mun wallahi da yanzu ina nan ina kwana a bakin bata.

"Matsalar ita ce ta wajen kwanciya saboda lokacin da ina aiki ina a gidan gwamnat, lokacin da gwamnati, lokacin da gwamnati ta bukaci gidanta dole ne in tashi in bata gidanta. Ni kuma ban yi tanadin gida ba, kin ga dole na hadu da kalubale na kuma hadu da matsala."

Da aka tambayeta game da dalilin da yasa bata tanadi komai ba duk da dadewar da tayi a harkar fim, Cima ta ce:

“Toh ai ni lokacin da na fara fim zuwa kawo yanzu, ban yi fim din da za a dauki N50,000 ko N30,000 ko N20,000 a bani ba balle nayi tanadi wani abu. Na je fim dinnan za a bani N5,000, N3,000.

Kara karanta wannan

Sarauniyar kyau mai Hijabi: An nemi na cire Hijabi don na ci nasara, amma na tubure

“Yanzu yau dinnan na je daukar fim wallahi N2,000 aka bani. Dubu biyun ce zan tara ta? Ina da baki bakwai a gabana wanda nike ciyarwa, mutum bakwai nake ciyarwa a kaina yadda kika ganni. A dubu biyun zan tara kudin da zan saya gida? Ba ni da shi."

Abun alherin da jarumi Ali Nuhu ya yi wa wata mai tallar awara, ya taba zukatan jama'a

A gefe guda, mun ji cewa duk da irin suka da kahon zuka da aka kafa wa jaruman masana'antar Kannywood, a wasu lokutan su kan yi abun jinjina da yabo.

Jaruman da suka fi samun yabo a wannan fannin sun hada da Hadiza Gabon, Ali Nuhu, Adam Zango da sauransu.

A nan jarumi Ali nuhu ne ya yi wani abun yabo da hali nagari da abokin aikinsa Abdul Saheer, wato Malam Ali na shirin Kwana Casa'in ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng