Jerin muhimman abubuwa 8 masu jan hankali da suka faru a masana'antar Kannywood cikin makon nan
- Kannywood na ɗaya daga cikin masana'antun dake jan hankalin mutane musamman a arewacin Najeriya
- Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa guda 8 da suka faru a masana'antar cikin mako ɗaya da ya gabata
- A wannan makon ne, mai ɗakin Jarumi Adam Zango, ta haifa masa ɗiya mace, wanda ya raɗa wa sunan mahaifiyarsa
Kano - Masana'antar shirya fina-finan hausa Kannywood na ɗaya daga cikin abunda ke jan hankalin mutane idan wani abu ya faru a cikinta.
Daga cikin wani abu mai jan hankali da ya faru a Kannywood cikin makon nan shine samun ƙaruwar da jarumi Adam Zango ya yi na ɗiya mace.
Fitaccen jarumin ya bayyana jin daɗinsa kuma ya raɗa wa jaririyar sunan mahaifiyarsa, kamar yadda Aminiya ta rahoto.
Bayan wannan, Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa 7 da suka faru a Kannywood cikin mako ɗaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Sarki Ali Nuhu bai taya Adam Zango murna ba
Kamar yadda muka sani, Jaruman Kannywood sun saba taya junansu murna ko akasin haka idan wani abu ya faru da ɗaya daga cikinsu a shafukansu na sada zumunta.
Sukan yi amfani da hoton wanda abun ya faru da shi, domin ta ya shi murna ko jajanta masa.
A binciken da muka yi a shafin Ali Nuhu, tun bayan samun ƙaruwar Adam A Zango zuwa yanzu, babu inda ya taya jarumin murna.
2. Sabon fim ɗin turanci a Kannywood 'Avengers'
Jaruman Hausa sun shirya wani fim da suka sanya wa suna 'Avengers' wanda aka shirya shi da yaren turanci, kuma ya ƙunshi zaratan Jaruman Kannywood.
Shirye-shirye sun yi nisa na fara nuna fim ɗin a gidan kallon Sinima dake Kano, wanda Bature Zambuk ya bada umarni.
3. Mansurah Isah ta koka kan halin da Najeriya ke ciki
Jaruma Mansurah Isah, ta koka kan yadda kowa yake yadda yaga dama a Najeriya, kuma komai yana ƙare wa ne a kan talaka.
A wani sakon bidiyo da ta wallaha, Mansurah ta koka kan yadda wahalhalun man fetur ke ƙara ta'azzara kuma kullum ƙara rufe gidajen mai ake yi.
A cewarta:
"Nasan akwai mai a gidajen mai da ake rufewa, suna haka ne domin wahal da talaka, Don Allah da wanne zamu ji? Kamar bamu da shugaban ƙasa kowa yana abinda ya ga dama."
4. An karrama Furodusa Usman Uzee a jami'ar Togo
Furodusa Usman Uzee ya samu karrama wa daga jami'ar Togo, inda ta bashi shaidar digiri na biyu.
Ɗaya daga cikin daraktocin Kannywood, Falalu A Dorayi, ya saka hotonsa tare da kalaman fatan Alheri, yace:
"Ina taya ka murna, Uzee bisa samun karramawa ta digirin digirgir daga Jami’ar Iheris da ke Togo.”
5. Nafisa Abdullahi ta bude sabon shago
Jaruma Nafisa Abdullahi, wacce ke haskawa a shiri mai dogon zango 'Labarina' ta buɗe sabon shagon kwalliya a Kaduna mai suna, 'Naf Cosmetics.'
6. Wasu jarumai sun tafi Umrah
Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun tafi aikin Umrah bayan buɗe Makkah a karon farko tun bayan ɓarkewar cutar COVID19.
Daga cikin waɗan da suka je Umrah akwai, Sadiq Sani Sadiq, Aisha Izzar So, Abdul Amart Mai Kwashewa da kuma AS Mai Kwai.
7. Almajirai sun kalli fim ɗin Fanan a Sinema
Jaruma Hadiza Gabon ta ɗauki nauyin Almajirai 40 su kalli sabon fim ɗin 'Fanan' a gidan Sinema na Platinun da ke kan hanyar Zaria a Kano.
Mansurah Isah, wacce ta ɗauki nauyin sabon fim ɗin, ita ce ta bayyana haka tare da wallafa hoton tare da yi wa Gabon godiya.
A wani labarin kuma Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema
Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin gini mai hawa 21 da yan uwansa kan gadon kudaɗe da motocin alfarma
Akwai wasu jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood da suka taba neman gwada sa'arsu a fagen siyasar Najeriya.
A wannan rubutun mun tattaro muku fitattun jarumai 5 da suka taba neman wata kujerar siyasa a yankunan su.
Asali: Legit.ng