Labaran duniya
Wani mutumi da ke zaune a Canada ya saki bidiyon wani gida a TikTok yana mai nunawa mabiyansa cikin gidan da yake zaune da iyalinsa. Yana biyan N778k duk wata.
Yayin da ake tsaka da rigima tsakanin sojojin Nijar da na Faransa, an fara tattunawa don bai wa sojin Faransa lokaci don tattare kayansu a hankali don ficewa.
Makarantu a kasar Faransa sun kori dalibai kusan 300 saboda karya dokar hana sanya hijabi da hukumomin kasar su ka yi ga dalibai musamman wadanda Musulmai ne.
Likitoci sun yi nasarar gano wani abun tiyata da aka bari a cikin wata mata lokacin da aka yi mata aikin haihuwa wata 18 da suka wuce. Girmansa ya kai faranti.
An bayyana bude iyakokin kasar Gabon bayan shafe kwanaki da rufe ta bayan yin juyin mulkin soja a makon da ya gabata. An abyyana dalilin yin juyin mulkin kasar.
Al’ummar Kenya sun jinjinawa wasu ma’aurata bakwai daga gudunmar Machakos kan yin auren hadin gwiwa. Ma’auratan sun ce sun yi hakan ne don ragewa juna zafi.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana fargabarsa kan juyin mulki da sojoji ke yi a Afrika. Ya bayyana dalilin da yasa amfani da sojoji ya zama matakin karshe a Nijar.
A ranar Alhamis ne kungiyar Tarayyar Afrika wato AU, ta sanar da batun dakatarwar da ta yi wa ƙasar Gabon biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi.
Birnin New York na Amurka ta ba da dama ga Musulmai su jiyar da kiran sallah a ranakun Juma'a da kuma lokacin watan Ramadan ba tare da neman izinin hukuma ba.
Labaran duniya
Samu kari