Duk da Tsagaita Wuta Trump Ya Sake Yin Babbar Barazana ga Iran

Duk da Tsagaita Wuta Trump Ya Sake Yin Babbar Barazana ga Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake aikawa da sakon gargadi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Donald Trump ya gargadi Iran kan ka da ta yi gigin tunkarar shingen da sojojin Amurka suka kafa don kulle tashoshin jiragen kasar
  • Shugaban na Amurka ya bayyana cewa duk jiragen yakin Iran da suka tunkari shingen, za a lalata su nan take

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya sake aikawa da sakon gargaɗi ga kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya yi gargadin cewa duk wani jirgin yaƙin Iran da ya yi ƙoƙarin tunkarar shingen ruwan da ya bayar da umarnin kafawa a kewayen tashoshin jiragen ruwan ƙasar, za a lalata shi.

Trump ya kara yin barazana ga Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Iran ta yi barazana kan sabon matakin da Amurka ta dauka

Ana kiran a mutunta yarjejeniya

Hakan na zuwa ne duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi na a girmama yarjejeniyar tsagaita wuta tare da komawa teburin tattaunawa.

Rundunar sojojin Amurka ta bayyana cewa za a fara wannan killace hanyoyin ne da misalin ƙarfe 14:00 GMT (ƙarfe 3:00 na rana agogon Najeriya) a ranar Litinin. Dokar za ta shafi dukkan jiragen da ke son fita ko shiga tashoshin jiragen ruwan Iran.

To sai dai, ko da yake lokacin da aka ɗiba ya wuce, har yanzu ba a ba da sanarwar fara aiwatar da matakin ba, kuma babu alamun an tare wani jirgi a halin yanzu.

Wace barazana Trump ya yi?

A sakon da ya wallafa, Trump ya bayyana cewa an riga an ruguza yawancin dakarun ruwan Iran a lokacin yaƙin.

Sai dai, ya ƙara da cewa idan wasu daga cikin abin da ya kira "jiragen yaƙi masu gudu" na Tehran suka kusanci shingen, "za a ruguza su nan take".

Kara karanta wannan

Trump ya gamu da matsala, Birtaniya ta juya wa Amurka baya a shirin killace Iran

Trump ya sanar da wannan killace hanyoyin ne bayan da tawagar da mataimakin shugaban kasa, JD Vance, ya jagoranta ta dawo daga tattaunawa da jami'an Iran a Pakistan ba tare da cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ba.

Trump ya gargadi kasar Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

A ranar Larabar da ta gabata, Amurka da Iran sun amince da tsagaita buɗe wuta na tsawon mako biyu domin ba da damar tattaunawa.

Tashar Channels tv ta ce masu shiga tsakani, wato Pakistan da Qatar, sun yi kira a ranar Litinin ɗin nan da a mutunta wannan yarjejeniyar yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya.

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya bayyana cewa:

"Har yanzu ana bin yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma kamar yadda nake magana a yanzu, ana yin dukkan ƙoƙarin da ya dace don magance matsalolin da suka rage."

Trump ya yi rashin nasara a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi rashin nasara a kotu.

Wani alƙali a Amurka ya yi watsi da ƙarar ɓata suna ta dala biliyan 10 da Shugaba Donald Trump ya shigar.

Donald Trump ya shigar da karar ne kan jaridar Wall Street Journal da Rupert Murdoch, game da wani labari da aka wallafa kan alaƙarsa da Jeffrey Epstein.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng