Muhimman Abubuwa 5 da Amurka da Iran Suka Gaza Warwarewa a Zaman Sulhu a Islamabad

Muhimman Abubuwa 5 da Amurka da Iran Suka Gaza Warwarewa a Zaman Sulhu a Islamabad

Islamabad, Pakistan - A makon da ya gabata ne kasar Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da ya shafe sama da wata guda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayan tsagaita wuta, kasashen sun yi zaman tattaunawa a birnin Islamabad na kasar Pakistan domin cimma matsayar sulhu da za ta kawo karshen yakin gaba daya.

Tattaunawar Amurka da Iran.
Harabar wurin da aka tsara tattaunawar sasanta Amurka da Iran a Islamabad Hoto: Pool
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa duk da Amurka da Iran sun fahimci juna a bangarori daban-daban, amma sun samu sabani a kan wasu sharudda masu muhimmanci.

An dai zauna teburin tattaunawar ne tsakanin wakilan Amurka karkashin jagorancin Mataimakin shugaban kasa, JD Vance da na Iran karkashin Ministan harkokin waje, Abbas Araghchi.

Wannan tattaunawa ta shafe kusan sa'o'i 24, daga yinin ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026 har zuwa daren Lahadi, kuma an tashi ba tare da cimma matsaya ta karshe ba.

Kara karanta wannan

Amurka ta gabatar da 'tayi na karshe kuma mafi kyau' ga tawagar Iran a teburin tattaunawa

Legit Hausa ta yi duba tare da tattaro muku muhimman abubuwan da aka samu sabani tsakanin Amurka da Iran duk da kokarin da mai shiga tsakani, Pakistan ta yi. Ga su kamar haka:

1. Shirin nukiliyar Iran

Shirin nukiliyar Iran na daya daga cikin manyan dalilan da Amurka ke ikirarin cewa sun haddasa wannan yaki a Gabas ta Tsakiya.

Amurka da Isra'ila sun sha bayyana cewa shirin kera makamin nukiliya da suke zargin Iran na yi, barazana ce ga tsaron kasashen, wanda a cewarsu shi ne dalilin daukar matakin soji.

Tawagar Iran
Tawagar Iran lokacin da ta kai ziyara ga Firaministan Pakistan, Muhammad Shehbaz Sharif Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Bayan tsagaita wuta a yakin, Iran ta bukaci ci gaba sarrafa sindarin Uranium a sharuddan ta mika wa Amurka, lamarin da ta bayyana a matsayin hakkinta.

A bangaren Amurka, ta bukaci Iran ta hakura gaba da sarrafa sinadirin na Uranium gaba daya, wanda ya sa aka gama tattaunawar Islamabad ba tare da cimma matsaya ba, kamar yadda AP News ta kawo.

2. Mashigar ruwa ta Hormuz

The Strait of Hormuz, wata karamar hanyar ruwa da ke yankin Iran, na daya daga cikin batutuwan da ba a cimma matsaya kansu ba a tattaunawar Amurka da Iran a Pakistan.

Kara karanta wannan

Bayan gama zagayen farko, an bayyana bukata 1 da Amurka ta amince za ta yi wa Iran

Iran ta kafa sharadin cewa ita za ta rika lura da wannan mashiga kuma za ta sanya haraji ga duk jirgin ruwan da zai wuce, yayin da Amurka ta kafe kan dole a bude hanyar ba tare da wani sharadi ba.

Rahoton New York Times ya nuna cewa mashigar ruwan na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya saboda akalla kaso 20 na man fetur din duniya yana wucewa ta wannan hanya.

Mashigar Hormuz.
Mashigar ruwa ta Hormuz da 20% na mai ke wucewa ta wurin Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tun bayan fara kai mata hare-hare a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026, Iran ta dauki matakin rufa maahigar, lamarin da ya sa farashin danyen mai ya tashi a kasuwar duniya.

3. Dakatar da hare-hare a Labanon

Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan mayakan kungiyar Hezbollah ta Lebanon duk da an tsagaita wuta, sun fusata kasar Iran, kamar yadda NBC News ta kawo.

Daga cikin sharuddan da Iran ta gabatar, ta bukaci a daina kai wa Hezbollah hari amma duk da haka Amurka ta nuna cewa babu wannan sharadin a yarjejeniyar tsagaita wuta.

Hezbollah dai ta fara kai hare-hare Isra'ila ne domin shigarwa Iran fada bayan barkewar yaki tsakaninsu, wanda hakan ya sa kasar ta Yahudawa ta maida martani.

Kara karanta wannan

An kammala tattaunawa ta farko, an ji yadda ta kaya tsakanin Amurka da Iran

Firaministan Isra'ila.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayin zantawa da manema labarai a birnin Jerusalem Hoto: Ronen Zvulum
Source: Facebook

4. Janye sojojin Amurka

Iran ta bukaci Amurka ta ba da tabbacin cewa ba za ta ƙara kai mata hari ba, sannan ta janye duka sojojinta daga yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya.

The Guardian ta ce wannan sharadi Amurka ba ta amince da shi ba kwata-kwata a tattaunawar da aka yi, amma ana sa ran kasashen biyu za su daidai lafin karewar wa'adin tsagaita wuta.

Haka zalika, Amurka ta bukaci Iran ta rage karfin sojojinta, wanda shi ma kasar Musulunci ta ki yarda saboda a cewarta, tana duk wani shiri ne don kare kanta.

5. Biyan diyya da cire takunkumi

Sakamakon shirin nukiliyan da ake zargin tana yi, Iran ta rika fuskantar takunkumi iri daban-daban daga Amurka da kawayenta, wanda ya jefa kasar cikin matsin tattalin arziki.

Haka zalika, a wannan yaki da ya dauki akalla kwanaki 40, an yi iran barna mai yawa, wanda hakan ya sa ta nemi a biya ta diyya sannan kuma a dage mata takunkumin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, an fara tattaunawa tsakanin Amurka da kasar musulunci ta Iran

Ministan Iran.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbad Araghchi a wani taro da ya halarta a Saudiyya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Majiyoyi na kusa da tawagar Iran a wurin tattaunawar da aka yi sun nuna cewa Amurka ta amince za ta cire takunkumin tattalin arziki a kan Iran, amma ta ki yarda da batun biyan diyya.

Matsalar da bukatun Amurka suka haifar

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Majalisar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi magana game da rashin samun daidaito da aka yi a zaman sulhu a Pakistan.

Ghalibaf ya ce tun kafin fara tattaunawar ya jaddada cewa Iran na da niyya mai kyau da kuma aniyar cimma matsaya.

Kasar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa buƙatun Amurka ne suka hana samun maslaha kan batutuwan mashigar Hormuz da fasahar nukiliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262