Yaki Ya Yi Tsanani: Kasashen Larabawa Sun Fara Kauce wa Taimakon Amurka

Yaki Ya Yi Tsanani: Kasashen Larabawa Sun Fara Kauce wa Taimakon Amurka

  • Kasashen Larabawa suna fara kauce wa Amurka wajen neman sababbin makamai, bayan hare-haren Iran sun rage musu kayan kariya
  • Kasashen sun fara komawa kasashe kamar Koriya ta Kudu, Ukraine da Birtaniya domin samun sabbin tsarin kariya, ciki har da makamai masu arha da jirage marasa matuka
  • Karancin samar da makamai a duniya, musamman a Amurka, ya sa wadannan kasashe ke neman hanyoyi daban, yayin da bukatar makamai ke karuwa sosai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudi Arabia - Bayan makonni shida na hare-haren sama masu tsanani, ana samun raguwar makamai a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majiyoyi suka ce makaman kariya daga hare-hare a Gabas ta Tsakiya sun ragu sosai, lamarin da ya sa kasashe suka fara neman karin makamai.

Yakin Iran da Isra'ila ya fara sauya salo a Gabas ta Tsakiya
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Yayin da ake da tsagaita wuta mai rauni tsakanin Amurka da Iran, ƙawayen Amurka a yankin suna duban duniya domin samun sababbi hanyoyin kariya cikin gaggawa, cewar The Wall Street Journal.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi babban matsalar Amurka a shirin yarjejeniyar zaman lafiya

Yadda yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin Donald Trump.

An fara kai hari ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 a birnin Tehran wanda ya yi ajalin mutane da dama tare da barnata wurare masu muhimmanci a kasar.

Harin ya yi sanadin mutuwa marigayi tsohon jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro wanda ya sauya salon yaki baki daya.

Daga bisani, Iran ta yi martani mai zafi inda ta kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila da Amurka wanda ya jawo wa ƙasashen asara mai yawa.

Kasashen Larabawa sun koma neman taimako wasu ƙasashe
Jagoran addini a Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Kasashen Larabawa sun fara neman mafita

Saudiyya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa suna komawa tsarin kariya na Koriya ta Kudu, jiragen Ukraine da bindigogin Gatling, tare da duba sababbin makamai daga kamfanonin Birtaniya.

Hakan ya nuna yadda hare-haren Iran suka girgiza kasashen Gulf, da kuma yadda jirage marasa matuki masu arha ke bai wa hare-hare damar kai wa da yawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kona coci da masallaci bayan hallaka Musulmi da Kirista 24

Rashin isasshen samar da makamai a duniya, musamman bayan yakin Ukraine, na iya sa masana’antun Amurka su rasa damar samun kwangiloli masu yawa nan gaba.

Kasashen Gulf suna ci gaba da neman sababbi hanyoyi, ciki har da hadin gwiwa da Ukraine da sauran kasashe, domin ƙarfafa tsaronsu cikin gaggawa da dorewa.

Kasashen Gulf suna ci gaba da neman sababbi hanyoyi, ciki har da hadin gwiwa da Ukraine da sauran kasashe, domin ƙarfafa tsaronsu cikin gaggawa da dorewa.

Iran ta koka kan game da tsagaita wuta

Mun ba ku labarin cewa mataimakin shugaban ƙasa na farko na Iran, Mohammad Reza Aref ya yi magana kan yiwuwar gudanar da yarjejeniya.

Aref ya ce sakamakon tattaunawar Islamabad zai dogara gaba ɗaya kan fifikon Amurka a tattaunawar zaman lafiya domin kawo maslaha a yakin da ake yi.

Ya bayyana cewa yarjejeniya mai amfani ga ɓangarorin biyu na yiwuwa idan Amurka ta mai da hankali kan muradunta na fifita kanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com