Bayan Susucewar Sulhu, Trump Ya kuma Yin Bazarana ga Iran da Kawayenta

Bayan Susucewar Sulhu, Trump Ya kuma Yin Bazarana ga Iran da Kawayenta

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yi sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan lalacewar sulhu
  • Trump ya ce rundunar ruwa za ta kulle mashigar Hormuz tare da dakile jiragen da suka biya Iran kudin wucewa bayan tattaunawa ta gaza
  • Shugaban ya bayyana cewa za a tare dukkan jiragen ruwa da ke shiga ko fita mashigar, tare da lalata bamabamai da Iran ta dasa domin tsaron hanyoyin ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya fusata bayan sulhun da aka shirya yi ya lalace a Pakistan.

Trump ya bayyana cewa rundunar ruwan kasar za ta fara kulle mashigar Hormuz tare da hana zirga-zirgar jiragen ruwa bayan tattaunawa ta gaza.

Trump ya yi barazanar rufe mashigar Hormuz
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds, Reza B.
Source: Getty Images

A sakon da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce nan take rundunar ruwan Amurka za ta fara dakile duk wani jirgi da ke kokarin shiga ko fita daga mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Bayan gama zagayen farko, an bayyana bukata 1 da Amurka ta amince za ta yi wa Iran

Barazanar da Trump ya yi ga Iran

Ya kara da cewa ya umarci sojojin ruwa su rika dakatar da duk jiragen ruwa a ruwan kasa da kasa da aka tabbatar sun biya Iran kudin wucewa.

Trump ya kuma bayyana cewa Amurka za ta fara lalata dukkan bamabaman da Iran ta dasa a mashigar domin kare hanyoyin ruwa daga barazana.

Ya yi gargadin cewa duk wani dan Iran da ya harba makami ga Amurka ko jiragen ruwa masu zaman lafiya zai fuskanci mummunar martani mai tsanani.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jiragen ruwa sun biya Iran kudin wucewa da kudin yuan na kasar China domin samun kariya yayin ketare mashigar mai muhimmanci.

Masu bincike sun ce rundunar IRGC ta Iran ta kafa tsarin karbar kudin wucewa inda ake tilasta jirage su bayar da bayanai tare da rakiyar tsaro.

Iran ta nuna yiwuwar sanya kudin wucewa ga dukkan jiragen ruwa a matsayin wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci a yankin.

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu da Iran, Shugaban Amurka zai ballo yakin da zai jefa kasashe a bala'i

Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaba Donald Trump a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Gargadin Donald Trump ga Iran

Trump ya taba gargadin Iran kan saka irin wannan haraji ga jiragen ruwa, yana mai cewa hakan ba zai amfanar da zaman lafiya ba.

Sanarwar kulle mashigar ta biyo bayan gazawar tattaunawar Amurka da Iran da mataimakin shugaban kasa, JD Vance ya jagoranta a Islamabad.

Vance ya ce Iran ta ki amincewa da sharuddan Amurka, yana mai cewa tattaunawar kai tsaye ta kare duk da yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu.

Trump ya ce duk da cewa an samu daidaito a wasu batutuwa, matsalar nukiliya ita ce babbar matsala da ta hana cimma wa yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu.

Ya kuma jaddada cewa Amurka ba za ta bari Iran ta ci gajiyar abin da ya kira haramtacciyar karbar kudin wucewa ba a mashigar Hormuz.

Trump ya magantu kan barazanar Iran a duniya

An ji cewa shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta fara "share" abubuwan da ke kawo cikas a mashigar ruwan Hormuz domin amfanin duniya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta karya sharudda 3 daga cikin yarjejeniyar sulhu da kasar Iran

Tattaunawa ta farko tsakanin Amurka da Iran ta kankama a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan ƙarƙashin jagorancin JD Vance da Mohammad Qalibaf.

Shugaban kasar Amurka dai ya yi ikirarin cewa yanzu barazana daya ce Iran take da ita yayin da ya ce an riga an kashe shugabanninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.