Shugaba Putin Ya Kira Takwaransa na Iran a Waya, an Ji Abin da Suka Tattauna Tsakaninsu

Shugaba Putin Ya Kira Takwaransa na Iran a Waya, an Ji Abin da Suka Tattauna Tsakaninsu

  • Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi magana da shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian
  • Putin ya ce ƙasarsa a shirye take ta shiga tsakani domin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya yayin da rikici ke ƙaruwa
  • Shugaban ya jaddada muhimmancin dakatar da yaƙi nan take, yana mai kira da a warware rikicin ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya maimakon amfani da ƙarfin soja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Moscow, Russia - Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya yi magana da shugaban Iran a wayar tarho game da yakin da ake yi.

Putin ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta shiga tsakani domin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Putin ya tattauna da shugaban Iran
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Anadolu Agency.
Source: Facebook

Wannan na zuwa ne bayan ya tattauna da shugaban Iran ta waya a yau Lahadi 12 ga watan Afrilun 2026, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi babban abin da ya hana samun daidaito tsakanin kasar da Amurka

Yadda yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin Donald Trump.

An fara kai hari ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 a birnin Tehran wanda ya yi ajalin mutane da dama tare da barnata wurare masu muhimmanci a kasar.

Harin ya yi sanadin mutuwa marigayi tsohon jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro wanda ya sauya salon yaki baki daya.

Putin zai shiga tsakani a yakin Iran da Isra'ila
Shugaban kasar Rashaz Vladimir Putin Hoto: Vladimir Putin.
Source: Getty Images

Putin ya magantu kan sulhun Iran da Amurka

Rahotanni sun nuna cewa Putin ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa da shugaban Iran Masoud Pezeshkian, inda suka duba halin da yankin ke ciki yayin da rikici ke ƙara ƙamari.

Putin ya nanata cewa dole ne a dakatar da faɗa nan take, yana mai jaddada cewa mafita mafi dacewa ita ce ta siyasa da diflomasiyya, ba amfani da ƙarfin soja ba.

Kara karanta wannan

An tashi baram baram: Amurka da Iran sun kasa fahimtar juna, ana iya komawa yaki

Haka kuma ya bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara yaɗuwa, yana mai cewa hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga yankin baki ɗaya da ma duniya.

Sanarwar ta ce:

“Vladimir Putin ya jaddada shirinsa na ci gaba da sauƙaƙa neman mafita ta siyasa da diflomasiyya ga rikicin, tare da shiga tsakani domin cimma zaman lafiya mai adalci da ɗorewa a Gabas ta Tsakiya."

Ƙasar Rasha na ƙoƙarin zama muhimmiyar mai shiga tsakani a rikicin, inda take tattaunawa da ƙasashe da dama ciki har da na yankin Gulf domin rage tashin hankali, cewar rahoton The Economic Times.

Matakin na Moscow na nuna ƙoƙarin ta na taka muhimmiyar rawa a diflomasiyya, yayin da ake ci gaba da fargabar tasirin rikicin ga tsaron yankuna da samar da makamashi a duniya.

Ana zargin ta aika jiragen yaki Iran

A wani labarin, mun ba ku labarin cewa a yayin da ake ci gaba da gwabza yakin Gabas ta Tsakiya, rahotanni sun fara zargin cewa Russia tana kai wa Iran dauki.

Wani rahoto ya yi zargin cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin na shirin aikewa Iran jiragen yaki marasa matuka.

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da ba Iran bayanan sirri, yana mai cewa yana da hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.