Iran Ta Fadi Dalili 1 da Ya Jawo Aka Tashi Baram Baram a Zaman Sulhu da Amurka

Iran Ta Fadi Dalili 1 da Ya Jawo Aka Tashi Baram Baram a Zaman Sulhu da Amurka

  • Kasar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa buƙatun Amurka ne suka hana samun maslaha kan batutuwan mashigar Hormuz da fasahar nukiliya
  • Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce ba su yi tsammanin cimma matsaya da Amurka a zama ɗaya ba saboda yanayin rashin amana
  • An rahoto cewa mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya bar Pakistan bayan sa'o'i 21 na tattaunawa ba tare da sanya hannu kan takarda ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun zargi Amurka da gindaya sharuɗɗan da suka wuce-gona-da-iri" yayin tattaunawar sulhu da aka gudanar a Pakistan.

A cewar kafofin yada labaran, bukatun Amurka da suka wuce makidi da rawa ne suka zama sanadiyyar rugujewar tattaunawar da aka gudanar a ƙarshen wannan mako a Islamabad.

Kara karanta wannan

An tashi baram baram: Amurka da Iran sun kasa fahimtar juna, ana iya komawa yaki

Iran ta dora alhakin rashin cimma matsayar sulhu kan batukun da Amurka ta gabatar da suka wuce gona da iri.
Ministan Pakistan, Muhammad Shehbaz Sharif ya gana da ministan wajen Iran Abbas Araghchi, kakakin majalisa Mohammad Baqir Qalibaf da wasu wakilai a Islamabad. Hoto: Handout/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta ce laifin Amurka ne a gazawar tattaunawarsu

A sanarwar da ta fitar a shafinta na Telegram, hukumar yaɗa labarai ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) ce ta sanar da cewa ɓangarorin biyu sun kasa samun matsaya a wannan zaman.

IRIB ta bayyana cewa an kasa samun matsaya kan muhimman batutuwa, ciki har da ikon kula da mashigar ruwan Hormuz da kuma haƙƙin Iran na ci gaba da bunƙasa fasahar nukiliya.

"Bayan sa’o’i 21 na tattaunawa da yunƙurin diflomasiyya, buƙatu na wuce-gona-da-iri daga Amurka sun hana cimma kowace irin yarjejeniya," in ji sanarwar.

Wannan martani ya fito ne jim kaɗan bayan da Amurka ma ta bayyana nata matsayar, inda ta ce Iran ta ƙi ba da tabbaci na dindindin kan daina kera makamin nukiliya.

Jim kaɗan bayan bayyana gazawar tattaunawar, Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya shiga jirginsa na Air Force 2 a Islamabad domin barin ƙasar Pakistan.

Kara karanta wannan

Iran ta gano karyar da Amurka ta sharara kan mashigar Hormuz, ta fadi 'gaskiya'

'Rashin amana' da saɓanin ra'ayi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa dama babu wani tsammani a birnin Tehran na cewa za a cimma yarjejeniya a halin yanzu, musamman a daidai lokacin da ake tsaka da yaƙi.

"An gudanar da wannan tattauna wa ne bayan kwanaki 40 na ƙaƙaba mana yaƙi, a cikin yanayi na rashin amana da zargi," in ji Baghae.

Kafar watsa labarai ta NBC News ta rahoto Baghae ya ƙara da cewa:

"A zahiri, bai kamata mu yi tsammanin za a cimma yarjejeniya a zama ɗaya kawai ba, kuma babu wanda yake da irin wannan tsammanin."
An tashi baram baram a tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan.
Dakin da aka gudanar da taron tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran a Pakistan. Hoto: Aamir QURESHI / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin tattaunawar ga muradin Iran

Duk da rashin cimma matsaya, Baghaei ya bayyana cewa an samu matsaya guda kan wasu batutuwa, sai dai akwai gagarumin saɓani kan wasu muhimman abubuwa guda biyu ko uku.

Ya bayyana tattaunawar a matsayin taro mafi tsawo da aka taɓa yi da Amurka a cikin shekarar da ta gabata, wanda ya haɗa da sababbin batutuwa kamar tsaron yankin teku da sauran matsalolin yanki.

Kara karanta wannan

"Ban da wuce gona da iri": Iran ta gargadi Amurka kan kutse ta mashigar Hormuz

Baghaei ya jaddada cewa a kowane hali, dole ne jami’an diflomasiyyar Iran su ci gaba da bin haƙƙoƙi da muradin al'ummar Iran, koda kuwa hakan na nufin tattaunawar za ta ɗauki tsawon lokaci ana gudanarwa kafin a ga amfaninta.

Amurka ta zargi Iran da lalacewar zaman sulhu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, JD Vance, ya sanar da cewa an tashi baram-baram a tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Iran ba tare da an cimma matsaya ba.

Amurka ta bayyana cewa ba za ta amince da kowace irin yarjejeniya ba muddin Iran ba ta ba da tabbacin daina kera makamin nukiliya na dindindin ba.

A ɓangare guda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa dama ba su yi tsammanin samun yarjejeniya a zama ɗaya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com